Connect with us

Labarai

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Published

on

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka Offor Foundation, a wani ɓangare na shirin ƙasa baki ɗaya na ƙarfafa horaswa da bincike a cibiyoyin lafiya na tarayya.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na cibiyar, Dakta Naziru A. Tukur ya fitar, ya ce tallafin na daga cikin wani babban shirin rabon littattafai da ya shafi cibiyoyin lafiya 58 da aka zaɓa a faɗin yankuna shida na ƙasar.

Dakta Tukur ya bayyana cewa an tanadi littattafan ne domin tallafa wa koyarwa, horas da ƙwararru da kuma bincike a cibiyoyin da suka amfana.

Ya ƙara da cewa gidauniyar ta ɗauki nauyin sayo da jigilar kwantena goma na littattafai da mujallu na zamani masu tsawon kafa 40 zuwa Najeriya domin aiwatar da shirin.

Wannan rabon littattafai shi ne karo na 13 na shirin da aka fara tun a shekarar 2013. Ba kamar lokutan baya ba, na shekarar 2026 ya mayar da hankali ne kacokan kan fannin kiwon lafiya.

A cikin wasiƙar da aka aika wa Daraktan Lafiya na cibiyar, Dakta Bello A. Mohammed, gidauniyar ta ce wannan tallafi ya biyo bayan buƙatar da Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a mai kula da harkokin daidaitawa, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya gabatar a madadin cibiyoyin lafiya na tarayya.

Wasiƙar wadda mukaddashin Babban Jami’in Ma’aikata na gidauniyar, Barista Chijioke James ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an amince da sayo da jigilar littattafan daga Amurka domin ƙara ƙarfafa horaswa a cibiyoyin lafiya na ƙasar.

Ta kuma nuna cewa Cibiyar ta Gusau na daga cikin cibiyoyin da aka zaɓa su ci gajiyar shirin.

Da yake mayar da martani, Daraktan Lafiya na cibiyar, Dakta Bello A. Mohammed, ya gode wa gidauniyar da kuma ministan bisa wannan tallafi na kan lokaci.

Ya ce gudunmawar za ta taimaka matuƙa wajen bunƙasa harkokin ilimi da ƙwarewa a cibiyar, musamman a daidai lokacin da ake ƙoƙarin mayar da ita asibitin koyarwa.

Dakta Mohammed ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni, ’yan kasuwa, ’yan siyasa, shugabannin addini da na gargajiya da sauran jama’a da su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki na taimako.

Ya jaddada cewa ci gaba da tallafi daga masu ruwa da tsaki yana da muhimmanci wajen haɓaka cibiyar da kuma inganta ayyukan kula da lafiya.

“Babu wanda ya kai talauci da ba zai iya bayarwa ba, kamar yadda babu wanda ya kai arziki da ba zai iya karɓa ba,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa za a yi amfani da littattafan yadda ya kamata domin inganta koyarwa da kuma ingancin ayyukan kiwon lafiya.

A gefe guda kuma, cibiyar ta kafa wani kwamiti domin tantance littattafan da kuma gano bukatun sassa daban-daban, domin tabbatar da an raba su yadda ya dace.

Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Shugaban Sashen Ayyukan Asibiti (Bincike da Horaswa), Dakta Usman Sulaiman, ya ce sun fara aikin tantance littattafan gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa za a rarraba littattafan bisa fannoni da muhimmanci, sannan a duba gibin da ke akwai a sassa da ɗakunan karatu daban-daban.

Ya ƙara da cewa kwamitin na shirin kafa tsarin bibiyar amfani da littattafan da kula da su, domin tabbatar da an kiyaye su yadda ya kamata kuma ma’aikata suna samun sauƙin amfani da su.

Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara