Labarai
An Warware Rikicin Shugabancin Da Ya Dabaibaye Kungiyar Likitocin Zamfara
Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara, Dr. Nafisa Muhammad Maradun, ta warware rikicin shugabancin kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Zamfara.
Jami’in yada labarai, ma’aikatar lafiya. Sulaiman Isa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce; Maradun tana magana ne a lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar dattawan kungiyar reshen jihar Zamfara karkashin jagorancin Dr. Hassan Mamman a ziyarar ban girma da ya kai.
Kungiyar dattawan ta yaba da jajircewar Dr. Maradun da hangen nesa wajen jagorantar kungiyar likitocin Najeriya ta jaha a wannan lokaci mai cike da kalubale.
Taron ya kuma yi tsokaci kan tasirin sa hannun ta ga kungiyar da kuma tsarin kiwon lafiya baki daya a jihar.
Dakta Nafisa Maradun ta jaddada fifikon inganta fannin lafiya bisa tsarin ceton lafiyar al’umma na Gwamna Dauda Lawal.
Ta nuna jin dadinta da ziyarar kungiyar dattawan tare da jaddada kudurin yin aiki kafada da kafada da kungiyar likitocin domin cimma manufofin shirin ceto.
Ziyarar na nuna wani gagarumin mataki na karfafa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar lafiya da kwararrun likitoci a jihar.
REL/AMINU DALHATU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
