Labarai
Hajj 2026: Jigawa ta Horas da Jami’an Alhazai na Kananan Hukumomi
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horas da masu horaswa (Train-the-Trainer) da suka fito daga ƙananan hukumomi 27 na jihar, domin shirya su kan yadda za su horas da maniyyatan jihar da ke shirin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.
Da yake jawabi a yayin taron horaswar na yini guda ga masu wa’azin yayin aikin Hajji na ƙananan hukumomi, Darakta Janar na hukumar ya bayyana cewa, an zabo su ne daga kananan hukumomi 27 na jihar domin aikin Hajjin da ke tafe.

Ya ce, waɗannan jami’an za su koma su horas da maniyyatan da ke shirin tafiya a cibiyoyin da aka tanada a ƙananan hukumominsu daban-daban a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa, an shirya taron ne domin wayar da kan jami’an kan nauyin da gwamnatin jihar ta ɗora musu.

A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da samun ingantaccen horo ga maniyyatan jihar kan muhimman ginshiƙai da ka’idojin aikin Hajji.
Labbo ya jaddada cewa, samun ingantaccen ilimi ga maniyyata zai taimaka musu wajen gudanar da aikin Hajji bisa koyarwar addinin Musulunci tare da zama jakadu nagari ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Daraktan Janar ya ƙara da cewa, taron zai ba maniyyatan damar sanin sahihanci da ingantattun ayyukan Hajji.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar za ta raba jami’an zuwa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da nasarar gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ƙara da cewa, a matsayinsu na jagororin maniyyata, wajibi ne su kasance kusa da maniyyatan domin ba su dukkan taimako da ake buƙata a Najeriya da kuma ƙasar Saudiyya.
Da yake tsokaci kan shirye-shiryen da ake yi, Daraktan Janar ya ce, hukumar ta riga ta karɓa tare da miƙa wasu daga cikin fasfofin ƙasashen waje na maniyyata domin samar da biza.

Ya yaba da yadda Gwamna Umar Namadi ya ɗauki nauyin kai masu horas da maniyyatan daga dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar zuwa ƙasar Saudiyya, yana mai bayyana hakan a matsayin abin a yaba.
Labbo ya shawarci mahalarta taron da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, yana mai cewa, hukumar ta samu gagarumar nasara a ayyukan Hajjin shekarar 2025.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ya ce, Masarautar Saudiyya ta bai wa Jihar Jigawa lambobin yabo daban-daban, ciki har da kyallen da ake lullube Ka’aba da shi, wanda ake kira Kiswa, da sauran kyaututtuka, waɗanda dukkansu aka miƙa wa Gwamna Umar Namadi a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
Tun da farko, Daraktan Wayar da Kai da Yaɗa Addini na hukumar, Alhaji Abdullahi Aliyu Hassan, ya yi jawabi ga jami’an kan nauyin da ke kansu a yayin ayyukan Hajjin shekarar 2026.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, masana da dama sun gabatar da takardu a taron, ciki har da Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure, Dr. Zakariyya Sa’idu Kandi, Malam Auwal Muhammad Ringim, Malam Isma’il Basirka da sauransu.
Wasu daga cikin mahalartan taron da suka yi magana da Rediyon Najeriya sun yaba wa Darakta Janar na hukumar, Ahmed Umar Labbo, bisa shirya taron.
Sun kuma yi kira ga maniyyata da su ba da haɗin kai domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
