Connect with us

Labarai

Gwamna Bago Ya Yi Alkawarin Kammala Duk Ayyukan da Ake Gudanarwa a Jihar Neja

Published

on

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sake tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan hanyoyi da ake aiwatarwa a fadin jihar.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake duba wasu manyan ayyukan hanyoyi a garin Bida.

Daga cikin ayyukan hanyoyin da Gwamna Umar Bago ya duba sun haɗa datagwayen hanyar Minna zuwa Bida, tsohon aikin gada na Titin legacy  da kuma gadar da ke haɗa hanyar Minna zuwa Abuja. Haka nan ya duba aikin hanyar zagaye mai tsawon kilomita 44 ring road da kuma gadar musayar hanya interchange bridge da ke Western Bypass na Bida.

An bayyana cewa idan aka kammala aikin ring road, zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa, musamman na manyan motoci masu ɗaukar kaya, da ke haddasa cunkoso a cikin garin Bida, tare da rage gurbatar muhalli da hatsarurrukan hanya. Gwamnan ya kuma duba tagwayen hanya mai tsawon kilomita 11, daga Bida Low Cost zuwa haɗuwa da Bida Western Bypass, wadda ta kai kashi 70 cikin 100 na kammala aiki.

Gwamna Umar Bago ya kuma duba hanyar da ke kaiwa fadar Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja.

Dukkan wadannan manyan ayyukan hanyoyi da Gwamna Umar Bago ya fara aiwatarwa na daga cikin sabbin tsare-tsaren sake gina jihar Neja, ƙarƙashin Ajandar Sabuwar Neja, da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.

PR / Aliyu Lawal

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara