Connect with us

Labarai

Hajj 2026: Jigawa ta Horas da Jami’an Alhazai na Kananan Hukumomi

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horas da masu horaswa (Train-the-Trainer)  da suka fito daga ƙananan hukumomi 27 na jihar, domin shirya su kan yadda za su horas da maniyyatan jihar da ke shirin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.

Da yake jawabi a yayin taron  horaswar na yini guda ga masu wa’azin yayin aikin Hajji na ƙananan hukumomi, Darakta Janar na hukumar ya bayyana cewa, an zabo su ne daga kananan hukumomi 27 na jihar domin aikin Hajjin da ke tafe.

Ya ce, waɗannan jami’an za su koma su horas da maniyyatan da ke shirin tafiya a cibiyoyin da aka tanada a ƙananan hukumominsu daban-daban a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa, an shirya taron ne domin wayar da kan jami’an kan nauyin da gwamnatin jihar ta ɗora musu.

A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da samun ingantaccen horo ga maniyyatan jihar kan muhimman ginshiƙai da ka’idojin aikin Hajji.

Labbo ya jaddada cewa, samun ingantaccen ilimi ga maniyyata zai taimaka musu wajen gudanar da aikin Hajji bisa koyarwar addinin Musulunci tare da zama jakadu nagari ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Daraktan Janar ya ƙara da cewa, taron zai ba maniyyatan  damar sanin sahihanci da ingantattun ayyukan Hajji.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar za ta raba jami’an zuwa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da nasarar gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ƙara da cewa, a matsayinsu na jagororin maniyyata, wajibi ne su kasance kusa da maniyyatan domin ba su dukkan taimako da ake buƙata a Najeriya da kuma ƙasar Saudiyya.

Da yake tsokaci kan shirye-shiryen da ake yi, Daraktan Janar ya ce, hukumar ta riga ta karɓa tare da miƙa wasu daga cikin fasfofin ƙasashen waje na maniyyata domin samar da biza.

 

Ya yaba da yadda Gwamna Umar Namadi ya ɗauki nauyin kai masu horas da maniyyatan daga dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar zuwa ƙasar Saudiyya, yana mai bayyana hakan a matsayin abin a yaba.

Labbo ya shawarci mahalarta taron da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, yana mai cewa, hukumar ta samu gagarumar nasara a ayyukan Hajjin shekarar 2025.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ya ce, Masarautar Saudiyya ta bai wa Jihar Jigawa lambobin yabo daban-daban, ciki har da kyallen da ake lullube Ka’aba da shi, wanda ake kira Kiswa, da sauran kyaututtuka, waɗanda dukkansu aka miƙa wa Gwamna Umar Namadi a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.

Tun da farko, Daraktan Wayar da Kai da Yaɗa Addini na hukumar, Alhaji Abdullahi Aliyu Hassan, ya yi jawabi ga jami’an kan nauyin da ke kansu a yayin ayyukan Hajjin shekarar 2026.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, masana da dama sun gabatar da takardu a taron, ciki har da Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure, Dr. Zakariyya Sa’idu Kandi, Malam Auwal Muhammad Ringim, Malam Isma’il Basirka da sauransu.

Wasu daga cikin mahalartan taron da suka yi magana da Rediyon Najeriya  sun yaba wa Darakta Janar na hukumar, Ahmed Umar Labbo, bisa shirya taron.

Sun kuma yi kira ga maniyyata da su ba da haɗin kai domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara