Connect with us

Labarai

Jigawa: Hukumar Alhazai ta Tunatar da Maniyyata Game da Muhimmancin Biyan Kudin Hadaya

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa tayi kira ga maniyyatan da su himmatu don biyan kudin hadaya na aikin hajjin bana.

Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka  yayin taron bitar sanin makamar aiki ga ma’aikata tare da sabbin jami’an alhazai na kananan hukumomin jihar.

Yana mai cewar, biyan kudin hadayan cikin lokaci na naira 270 yana da muhimmaci domin cimma nasarar aikin.

Labbo ya kuma yi kira ga ma’aikatan hukumar da sabbin jami’an alhazai na kananan hukumomi 27 da su zamo masu tsoran Allah SWT yayin gudanar da aiyukan su gami da sauke nauyin da ya rataya a kansu a nan gida da kuma kasar Saudiyya.

Da ya waiwayi batun hakuri da maniyyata kuwa, Darakta Janar din yayi kira a gare su da su kasance masu hakuri tare da nuna juriya wajen tafiyar da al’amurran maniyyatan jihar.

Shi ma a nasa jawabin, Darektan tsare-tsare na hukumar, Alhaji Muhammad Garba ya ce akwai kwamitoci da dama da hukumar za ta kafa don cimma burin da aka sanya a gaba.

Ya kara da cewar, wajibi ne sabbin jami’an su rika halartar bita a cibiyoyin yankunansu domin fara sanin dukkan maniyyatan dake karkashin kulawar su.

Mohammad Garba, ya yi kira ga sabbin jami’an da su tabbatar da kula da lafiya da bada abinci da sa ido a masaukin Alhazai a Makkah da Madina da Arafat da mmMuna da sauran dukkan abubuwan da suka shafi Alhazai.

Babban limamin masallacin 744 dake Dutse kuma Sa’in Dutse, Malam Muhammad Yunusa yayi bayani mai tsawo kan muhimmacin aikin hajji.

Yana mai kara kira a gare su dasu maida hankali wajen halartar bita don sabawa da Alhazai tare da kara sanya ido akan mata kan yadda suke gudanar da aikin su a kasa mai tsarki.

Mahukunta hukumar sun gabatar da bayanai da dama kan ayyukan da suka shafi jami’an Alhazai da yadda ake dakile matsaloli idan bukatar hakan ta taso.

Daga bisani an baiwa sabbin jami’an kananan hukumomi 27 wato centre officers takardar nadin da aka yi masu na kula da walwala da jin dadin Alhazai.

Wasu daga cikin sabbin jami’an sun yabawa Gwamna Umar Namadi bisa nada su a matsayin jami’an kananan hukumomi tare da biya masu kudin  hadaya.

Sun kuma jinjinawa Darekta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa karamcin da yake nuna masu wajen shirya taron sanin makamar aikin daya rataya a wuyansu.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara