Connect with us

Labarai

INEC Ta Kaddamar da Mataki na Biyu na Rijistar Masu Zabe Kai Tsaye a Sokoto

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kawo aikin rijistar masu zabe kusa da talakawa a Jihar Sokoto, tare da kaddamar da mataki na biyu na aikin Rijistar Masu Zabe Kai Tsaye (Continuous Voter Registration – CVR), wanda aka tsara domin saukaka samun damar rijista ga dukkan waɗanda suka cancanta a fadin jihar.

Da yake bayani kan aikin, Kwamishinan Zabe a Sokoto, Umar Yusuf Garba, ya ce aikin, wanda ya fara ranar 5 ga Janairu, 2026, zai ci gaba har zuwa 17 ga Afrilu, 2026, kuma an tsara shi ne domin rage wahalar tafiya mai nisa ga mazauna, musamman ma waɗanda ke zaune a kauyuka, ta hanyar sauƙaƙa rijistar a matakin ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa wannan sabon mataki ya biyo bayan nasarar kammala mataki na farko, wanda ya gudana daga 18 ga Agusta zuwa 10 ga Disamba, 2025, inda Jihar Sokoto ta zama ta uku mafi kyawun aiki a ƙasa baki ɗaya.

A cewar Kwamishinan, an samu nasarar rijistar jimillar masu zabe 162,299 a mataki na farko, abin da ya nuna karuwar wayar da kan jama’a kan hakkinsu na zabe a jihar.

Ya ƙara da cewa mataki na yanzu zai baiwa ‘Yan Najeriya damar da suka kai shekaru 18 yin rijista, maye gurbin katunan zabe da suka ɓace ko lalace, gyara kurakurai a bayanan masu zabe, da kuma canja rijista daga wuri zuwa wuri a cikin ko wajen jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa rijistar na gudana a lokaci guda a dukkan ofisoshin INEC na kananan hukumomi 23, ofishin jihar, da sauran wuraren da aka amince da su a fadin Sokoto.

Ya sake jaddada kudurin INEC na gudanar da aikin rijistar masu zabe cikin gaskiya, adalci da inganci, domin ƙarfafa dimokuradiyya daga tushe.

NASIR MALALI

 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara