Labarai
Zamfara: Ulama Sun Ta’a;;aka Karuwar Ta’addanci da Shaye-shaye
Ƙungiyar Malama Jihar Zamfara (Zamfara State Ulama Consultative Forum) ta danganta yawaitar ta’addanci da aikata miyagun halaye a cikin al’umma da amfani da miyagun ƙwayoyi musamman tsakanin matasa, inda ta bayyana hakan a matsayin babban abin da ke haifar da lalacewar tarbiyya.
Shugaban Ƙungiyar, Sheikh Umar Bin Kanoma, ya bayyana haka yayin da yake yi wa ‘yan jarida bayani a Gusau, babban birnin jihar, a ƙarshen taron Ƙungiyar.
Sheikh Kanoma ya ce taron ya fara da addu’o’i da ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, gwamnatin Jihar Kano, da kuma dukkan ‘yan Ummatul Muslima, dangane da mummunan lamari da ya faru a Kano kwanan nan.
Ya bayyana cewa an tattauna sosai kan karuwar tashin hankali da miyagun halaye a cikin al’umma, musamman a cikin al’ummar Musulmi, bayan kisan mai tsanani da aka yi wa uwa da yara shida a Kano, wanda Ƙungiyar ta yi tir da shi sosai, tana mai cewa abin ya tayar da hankali, ba abin yarda ba ne, kuma yana da matuƙar damuwa.
A cewar Sheikh Kanoma, amfani da miyagun ƙwayoyi yana wuya wa zuciya, yana canza halayyar mutum, kuma yana haifar da aikata laifuka masu tashin hankali.
Ƙungiyar ta yi kira ga malamai da limamai da su ƙara mayar da hankali wajen koyar da tarbiyya ta hanyoyi daban-daban kamar hudubobi, darussa, da sauran tashoshin wayar da kai, tare da jaddada kyawawan halaye, zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.
Sheikh Kanoma ya kuma yi kira ga shugabannin addini da su ƙarfafa aikin wayar da kan jama’a game da miyagun halaye, tare da hana kafa da gudanar da wuraren sayar da miyagun ƙwayoyi.
AMINU DALHATU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
