Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Kashe Naira Biliyan 3 Wajen Gina Azuzuwa A Makarantu

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin  ta na kashe sama da Naira biliyan 3 wajen gina sabbin azuzuwa a fadin kananan hukumomin jihar 44.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati dake Kano.

Ya ce gwamnati na da burin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa ta hanyar gina karin ajujuwa da gyara wadanda suka lalace.

Gwamnan ya bayyana cewa za a dauki sama da jami’an tsaro 17,000 aiki a fadin jihar domin tabbatar da tsaron kayayyakin makarantun firamare, inda za a tura mutum 400 a kowace karamar hukuma.

Za a dauki masu gadi a yankunan da suke domin aiki a makarantun firamare da nufin tabbatar da ganin an kare makarantun yadda yakamata“.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa kowace karamar hukuma za ta samu Naira miliyan 25 domin gyara azuzuwa, inda hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa za ta sa ido kan aikin domin tabbatar da ingancisa.

Ya kara da cewa zuba jarin ya nuna kudirin gwamnati na inganta ababen more rayuwa da samar da ingantaccen ilimi  ga dalibai.

 

Abdullahi Jalaluddeen

 

Labarai

Labarai7 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara