Connect with us

Ilimi

Uwargidan Gwamnan Jihar Kwara Ta Bukaci Dalibai Su Kauracewa Shaye-shaye

Published

on

Uwargidan gwamnan jihar Kwara, Ambasada Olufolake AbdulRazaq, ta shawarci dalibai da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, tare da gujewa dukkan wani nau’in tu’ammali da kwaya.

Uwargidan gwamnan ta bayar da wannan shawarar ce a makarantar sakandiren Sarauniya Elizabeth da ke Ilorin a yayin wani taron da kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kwara da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da ofishin uwargidan gwamnan jihar suka shirya, domin  wayar da kan dalibai a jihar, a bikin ranar yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana.

Uwargidan gwamnan wadda kwamishinar lafiya ta jihar Dr Amina Ahmed El-Imam ta wakilta,
ta jaddada mahimmancin dalibai su zama jakadu nagari ta hanyar gujewa miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ba su dace ba.

Ta kuma yi kira ga daliban Makarantu da su wayar da kan sauran daliban game da illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da gujewa cin zarafi ko yaudarar su da shan miyagun kwayoyi.

Uwargidan gwamnan, ta bayyana irin jajircewar da gwamnatin jihar ta yi na ganin  ta kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai.

Ta kuma bukaci daliban da su bai wa ilimi fifiko, inda ta kara da cewa ilimi shi ne abu mafi daraja da za su samu.

Ambasada  Olufolake AbdulRazq ta kara karfafawa daliban kwarin guiwa da su mai da hankali kan karatunsu tare da kaurace wa duk wani abu da zai illata rayuwarsu.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara