Ilimi
Gwamnan Jihar Kwara Ya Bukaci Kafafen Yada Labarai Su Rika Aiki Da Kwarewa
An shawarci kwararrun kafafen yada labarai da su yi la’akari da kishin kasa a cikin rahotannin da suke bayarwa don inganta al’umma.
Gwamna ,AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya ba da shawarar a cikin sakonsa wajen makon ‘yan jarida nab ana da aka gudnaar a Ilorin babban birnin Jihar.
Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin babban sakataren yada labaran sa Rafiu Ajakaye ya ce ya kamata kafafen yada labarai su kiyaye dabi’ar aikin jarida.
Ya ce bai kamata a gurgunta karfin da kafafen yada labarai ke da shi na sauya al’amura da kyau ba.
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana fatan cewa sabon ajandar fatan da gwamnati ke ciki zai kyautata rayuwa ga talakawa.
A cikin jawabinsa sashen masu aiko da rahotanni na kungiyar ‘yan jarida a jihar Kwara Mallam Abdulhakeem Garba , ya bada tabbacin cewa kwararrun kafafen yada labarai za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen baje kolin ayyukan a cikin al’umma kamar yadda suka tabbatar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kwara da ta shirya rangadin da ‘yan jarida za su yi a kafafen yada labarai domin ba su damar bayar da rahoton ayyukan ci gaba a yankunan karkara.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban kwamitin shirya makon manema labarai na NUJ, 2025, Mista Demola Akinyemi ya bayyana shirya shirin a matsayin gata da ba kasafai ake samun sa ba.
Ya mika godiyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki da suka goyi bayan taron wanda ake gudnaarwa duk shekara.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai1 day agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
