Labarai
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar.

Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da watanni 12 masu zuwa.

Malam Umar Namadi ya kara da cewar, an bada aikin sanya kwaltar ne da kuma sauran ayyukan inganta hanyoyi domin saukakawa manoma da sauran al’umma harkokin sufuri.

A don haka, ya yi kira ga al’ummar jihar da su rinka sa ido akan kayayyakin da hukuma ta samar musu domin gudun lalacewa da kuma barnatarwa.

A jawabinsa na maraba, kwamishinan ayyuka na Jihar, Injiniya Gambo S Malam ya ce gwamnatin jihar, ta bada ayyukan hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, bikin ya samu halartar Ministar ma’aikatar Ilmi Dr. Suwaiba Ahmed Babura da Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori da kakakin majalissar dokokin jihar Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da manyan jami’an gwamnatin jihar.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai1 day agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
