Connect with us

Ilimi

Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa

Published

on

Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku.

Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sashen ilimi.

Da take jawabi a wajen taron, Minista a ma’aikatar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Sa’id ta bayyana cewa, a ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi na ƙarfafa tsarin ilimi, ya amince da kashe Naira biliyan 120 don bunƙasa shirin fasaha da koyon sana’o’i (TVET) a Najeriya.

Ministar ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 40 domin kammala aikin ɗakin karatu na ƙasa da aka yi watsi da shi, domin tallafawa bincike da cigaban karatu.

Farfesa Suwaiba ta ƙara da cewa, ma’aikatar ilimi ta tarayya ƙarƙashin jagorancin Minista Alausa ta ƙaddamar da Shirin Sabunta Hanyar Ilimi ta Najeriya (NESRI).

Ina da burin mayar da Najeriya daga tattalin arzikin da ke dogara da albarkatu zuwa tattalin arzikin da ke dogara da ilimi, tare da rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta, rage ƙarancin koyo, da samun  ƙara ƙwarewa.”

Yayin da yake buɗe taron, Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana nasarorin da sashen ya samu, inda ya ce ya samar da manyan mutane kamar ministocin ilimi biyu, shugabannin jami’o’i tara, da matan gwamnan jihar Kano guda uku, da sauran fitattun ’yan Najeriya da suka yi fice a fannoni daban-daban.

Yayin da yake yabawa taken taron da dacewarsa, Farfesa Sagir ya tabbatar da cewa jami’ar tana nan daram wajen tallafawa duk wani shiri da zai ɗaga matsayin ilimi zuwa na ƙasa da ƙasa.

A jawabinsa na maraba, Shugaban tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero Kano (BUK), Dakta Abubakar Ibrahim Hassan, ya jaddada yadda tsangayar ke  kokari wajen shirya harkokin ilimi da na kimiyya.

Daga cikin nasarorin da Jami’ar BUK ta samu a kwanan nan akwai samun tallafin TETFUND guda biyu da kowanne ya haura naira biliyan 30, tare da lashe wani shirin koyar da harsuna biyu wanda Bankin Raya Musulunci da Hukumar Ilimin Firamare ta Kasa (UBEC) suka dauki nauyi.”

Taron ya yi armashi inda aka bayar da lambar yabo ga fitattun ‘yan Najeriya da suka hada da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa Farfesa Hafsat, da Minista a ma’aikatar Ilimi ta Jiha Farfesa Suwaiba, tsohuwar Ministar Ilimi Farfesa Rukayya, da Farfesa Isah Yahaya Bunkure da wasu da dama.

Daga Khadija Aliyu 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara