Ilimi
An Bukaci Ayi Gyara A Manhajar Ilimin Kasan Nan.
Babban limamin Bauchi ya yi kira da ayi gyara a manhajar tsarin ilmi don dakile rashin aikin yi a tsakanin dimbin matasa a kasar nan
Alhassan Usman Bauchi
Babban Limamin Masallacin Bauchi, Imam Bala Ahmad Baban-Inna, ya bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da su gyara manufofin ilimi game da horar matasa sana’o’i don magance matsalar rashin aikin yi a fadin kasar.
Imam Ahmad Baban Inna ya yi wannan kiran ne a cikin hudubarsa jim kadan bayan ya jagoranci raka’o’in biyu na Sallar Idi karama wadda aka gudanar babban Massalaci Idi na Bauchi da ke Kofar Idi a cikin a cikin garin Bauchi.
Babban Limamin Bauchi, kenan Imam Ahmad Baban Inna lokacin da ya ke ya jagorantar Sallar idi karama mai Raka’o’i biyu don kawo karshen azumin watan Ramadan na wannan shekarar ta 2026.
A cikin hudubarsa, Imam Baban-Inna ya lura cewa da yawa daga cikin waɗanda suka kammala karatun ba sa samun aikin gwamnati, yana mai kira ga mutane masu hannu da shini da su zuba jari a cikin kamfanoni na halal waɗanda za su iya ɗaukar dumbin matasa aiki kana ya yi bayanin cewa yawan jama’a na buƙatar tsari da ƙwarewa wajen koyo da samar da sana’o’i don dogaro da kai.
Ya shawarci Musulmai da su nemi taimako daga Allah SWT maimakon roƙon mutane kana yayi kira ga masu kuɗi a cikin al’umma da su guji rowa da kuma yin karimci wajen kura da bukatum al’umma don samun rahamar Allah.
Babban Limamin wanda ya bayyana cewa shan miyagun ƙwayoyi ya zama babban matsala a duniya wadda ke haifar da barazana ga al’ummar zamani ta hanyar lalata lafiyaĖr jiki da dai-daita iyalai da kuma ƙarfafa ƙungiyoyin ta’adanci ya shawarci iyaye da su sanya ido kan ‘ya’yansu don kare su.
Ya baiwa Musulmi kwarin gwiwa da su riƙe darussan da suka koya da aiki dashi cikin watan Ramadan don samun yardar Allah SWT .
Wani Mashhurin Malamin Addinin Musulunci a Bauchi Imam Akibu Iliyasu wadda ya nuna gidiyar ga Allahu S.W.T da ya nuna wa musulimi karshen watan Azumin Ramada cikin aminci duk da matsin Tattalin arziki da ake fama da shi, ya yi karin haske ga me da muhimmamci wannan rana ga Musulmi.
A cikin sakonsa, Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Dr. Rilwan Suleiman Adamu, wanda ya yaba wa dukkanin malaman Musulunci da suka gudanar da Tafseerin Alƙur’ani na wannan shekarar cikin lumana, ya yi kira ga Musulmi da su hada kuma kada su yi kasa a gwiwa wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kasar nan.
Ana shi bangaren Gwamna Bala Muhammad ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci wajen gudanar da addu’o’in zaman lafiya da kawo karshen ta’dacin ga al’ummomin da Gwanna, Digare, Yalo da Mansur duk a karamar hukumar Alkaleri da ayyukan ‘yan ta’adda ya dai dai su
Dubban Musulmai ne dai daga fadin jihar ciki har da Gwamnan da Sarkin Bauchi da manyan jami’an gwamnati da dattawan garin Bauchi da Malaman Musulunci da shugabannin gargajiya da na al’umma da dai sauransu, suka halarci sallar Idin.
Radiyon Najeriya ya lura cewa bikin wanda aka gudanar karkashin kulawar tsaro na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da kevfadin jihar ya gudana cikin lumana a dukkan kananan hukumomi ashirin na jihar.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai7 days agoGwamnatin Kano ta Samar da Babura Don Inganta Yaki da Cutar Tarin Fuka a Karkara
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
