Labarai
Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila
Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon da ya gabata, sakamakon rashin bin umurninta na kaucewa kai hare hare a birnin Rafah dake kudancin Gaza.
Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Antoni Guterese ya ce babban kuskure ne mamayar da israila ta kai Rafah, la’akari da cewa an kasa amfani da hanyoyin da aka saba bi wajen isar da kayakin agaji, haka ma tuni aka rufe hanyoyi 2 mafi sauki da a ke bi dan shigar da kayayyaki cikin Gaza.
A jiya Talata ne rahotanni suka bayyana cewa bangarorin da ke rikici da juna sun amince da komawa kan teburin sulhu, domin tattauna batun tsagaita wuta tare da kawo karshen yakin na Israila da Hamas.
Rundunar sojin Israila ta ce tun da sanyin safiyar ranar Talata ne dakarunta suka kwace ikon kan iyakar mashigin Rafah bayan hare haren sama da suka shafe tsawon lokaci suna yi, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 27.
Ita ma Hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta ce a kowace rana Falasdinawa da dama na fuskantar barazanar rasa rayukansu saboda hana kayayyakin agaji shiga inda suke da Israila ta yi.
Akalla Falasdinawa dubu talatin da hudu da dari bakwai da tamanin da tara ne sojojin Israila suka kashe tun bayan barkewar yaki a cikin watan Oktoban shekarar 2023 yayin da wasu dubu saba’in da takwas da dari biyu da hudu suka jikkata.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
