Labarai
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki Da Dama A Karamar Hukumar Bodinga
Daruruwan iyalai da manoma sun shiga cikin muwuyacin hali sakamakon iftila’in ambaliya da ta afka a kauyen Badau da ke gundumar Darhela da Butuku a gundumar Toma, ƙaramar hukumar Bodinga a jihar Sakkwato.
Ambaliyar ta nutse da dubban gonaki, ta rusa gidaje, tare da lalata kasuwar garin Dandin-Mahe da ke cikin ƙaramar hukumar Shagari, abin da ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali.

A cewar rahoton farko, sama da gonaki 3,000 ne suka lalace a Badau, yayin da gonaki 75 suka lalace a Butuku.
Bisa ga rahoton hukumar ƙaramar hukumar Bodinga, tawagar haɗin gwiwa daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) da Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ofishin Sakkwato, sun kai ziyara yankunan da lamarin ya shafa domin tantance irin asarar da aka yi.

Jagoran tawagar shi ne Daraktan Tallafi da Sake Gina Rayuwa na SEMA, Malam Mustapha Umar, tare da jami’in tsare-tsare na NEMA a Sakkwato, Mista Tukur Abubakar.
Rediyon Najeriya a Sakkwato ya ruwaito cewa iftila’in ya biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka kwashe kwanaki huɗu ana yi lokaci zuwa lokaci a yankin.

Mazauna yankin sun roƙi gwamnatin jiha da ta tarayya da su kawo tallafin gaggawa domin rage musu ƙuncin da suke ciki.
Tawagar SEMA da NEMA sun tabbatar wa mazauna yankin cewa za su tattara bayanan da suka tara domin gabatar wa ga hukumomi don hanzarta kawo agajin gaggawa.

Tawagar ta kuma kai ziyara wasu yankuna a cikin ƙaramar hukumar Shagari inda ambaliyar ta shafi ƙauyuka huɗu, tare da lalata kasuwa da gonaki 74, da kuma jawo asarar gine-gine.
Har ila yau, wani gida ya rushe sakamakon ambaliyar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yaro mai shekaru bakwai mai suna Jafar Sani.
Daga Nasiru Malali
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
