Connect with us

Labarai

Alhazai Za Su Biya Miliyan Bakwai Don Sauke Farali

Published

on

Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bukaci maniyyatan aikin Hajjin bana da su biya karin Nera Miliya Daya da Dubu Dari Tara kan kudaden da suka biya a baya.

Hakan na kunshe ne  cikin wata sanarwa da ta fito  da yammacin ranar Lahadi mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara.

Fatima Usara ta kara da cewa  hukumar ta kuma bada wa’adin  ranar 29 ga Maris a matsayin ranar da za a kammala bada cikon kudin.

Ta ce hakan ya zama wajibi duba da yadda darajar Naira  ke faduwa a kowacce rana.

A baya dai hukumar ta tsayar da naira miliyan 4 da dubu dari 5 a matsayin kudin aikin Hajjin, kafin daga bisani ta kara naira dubu dari 4, ya zama naira miliyan hudu da dubu 9, sai kuma yanzu da ta sanar da karin kusan naira miliyan biyu.

Idan har wannan kari ya tabbata a yanzu, farashin kujerar aikin hajji zai tashi kan Naira miliyan 6 da dubu dari 9.

A watan Fabarairun da ya gabata ne Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta kayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kudin kuejrar hajjin bana.

 

Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar kara wa maniyyatan kudi bisa dalilan faduwar darajar naira.

Labarai

Labarai12 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara