Ilimi
Bukin Sallah: Mai Martaba Sarkin Kauru Ya Bukaci A Ba Mata Dama Su Nemi Ilimi
Mai martaba Sarkin Kauru ta jihar Kaduna Alhaji Zakari Ya’u Usman ya bukaci jama’ ar yankin su hada kai suyi aiki tare don dakile matsalar tsaron da yankin ke fuskanta a yanzu.
A sakon sa na barka da sallah a fadarsa da ke Kauru, Mai Martaba Sarki ya nuna matukar famuwarsa akan matslaar masu garkuwa da mutane da ke kara habaka da satar amfani gona da wasu ayukkan badala a wannan yankin.
Alhaji Zakari Ya’u ya zayyano irin kalubalen da wannan matsalar ke haifarwa tsakanin al’umma tare da kira da kakkausar murya na a dauki matakin maganinta gaba daya.
Ya Kuma bayyana irin mahimmancin hadin kan al’umma akan wannan don kawo karshensa sannan ya umurci dukkanin masu rike da sarautu suyi aiki da mutanensu tare da jami’an tsaro don samo hanyar dikile wannan muguwar ta’ada.
Mai Martaba Ya’u na II yace akwai bukatar hada karfi da karfe wajen Kare rayuka da dukiyoyi da kuma fitar da al’umma daga wannan sabuwar matsala.
Bugu da kari Banda maganar tsaro, mai martaba ya kuma tabo tare da bayyana muhimmamcin kula da ilimin ‘ya’ya mata tare da Kiran a kara basu dama suje makaranta.

Sarkin Kauru Zakari Ya’u Usman II da Malam Yusuf Zubairu (Tambarin Kauru)
Sannan yayi bayanin cewa gudummuwar da ilini ke bayarwa wajen ba jama’a damar dogara DA Kai da Kuma habakar tattalin arzikin da ci gaba.
Sannam mai Martaban bai tsaya nan ba sai da kawo irin mahimmancin da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samarawa mabanbantan al’umma don haka ya bukaci a hada kai ayi aikin bunkasa yankin Kauru.
Ya Kuma jawo hankalin al’ummarsa game da mahimmancin zuwa asibiti don duba lafiya.
Radio Nigeria kaduna ya bada labarin cewa sakon mai martaba na sallah karama ya nuna irin yunkurin da yake wajen maganin matsalolin da jama’ar masarautar ke fuskanta, inda ya bayyana aiki tare ta bangaren ilimi, zaman lafiya da harkokin kula da lafiya a matsayin jigon ci gaban da ake bukata.

Sakataren masarautar Kauru, Mal Muhammad Sani Suleiman, (Dan’s buran Kauru)
Hakama Sakataren masarautar Kauru Malam Muhammad Sani Suleiman (Dan Buran Kauru) ya mika sakonsa na taya murna ga mi martaba Sarki Kauru game da cikar sa shekara 3 akan mulki.
Sakon Dan Buran na Kauru ya nuna irin godiya da yadda tsarin shugabancin mai martaba da irin gudummuwar da ya ke bayarwa ga bunkasar al’ummar yankin a wadannan shekarun 3.
Yusuf Zubairu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
