Labarai
Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki.
Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni.

Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba.
Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari fili domin yin karin gine gine a asibitin.
Tunda farko a nasa jawabin, Babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura yace sun kai ziyarar ce domin gabatar da kansu da kuma neman karin hadin kai da goyan bayan gwamnatin jihar wajen ci gaban asibitin.

Dr. Salisu Babura ya shedawa Gwamnan ma’aikatan asibitin da gwamnatin tarayya ke biyan albashi sun kai 877.
Ya kuma yi nuni da cewar cikin adadin, guda 250 sun fito ne daga jihar jigawa.
Kazalika, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyan bayan da ke baiwa asibitin.

Yana mai fatan kara bullo da wasu hanyoyi domin magance kalubalen da ke fuskantar asibitin a yanzu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
