Connect with us

Kasuwanci

Kungiyar ‘Yan Dako Reshen Jigawa ta Kaddamar da Sabon Shugaba

Published

on

Daga Usman Mohammed Zaria

Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse.

A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da ya’yan kungiyar tare da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar da ake bukata.

Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci masu sana’ar dako a karamar hukumar Dutse da su nuna cikakken goyon baya ga sabon shugaban, tare da mutunta ‘yan kasuwa a matsayin su na jigo wajen ciniki da kasuwanci wanda ke bude kofar samu ga ‘yan dako.

Ya kuma yi addu’a ga marigayi mai martaba sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi, inda ya bukaci sarki Muhammad Hameem Nuhu Sanusi ya ci gaba da aiki da kyakkyawan tarihin da tsohon sSarkin  bari wajen mu’amala mai kyau da shugabanci nagari da kuma adalci ga talakawansa.

Ya kuma bayyana kudurin kungiyar na aiki tare da masu ruwa da tsaki domin inganta harokokin saye da sayarwa a jihar Jigawa, inda ya bukaci gwamnatin jihar da ta bada kulawa ta musamman wajen bunkasa ciniki da masana’antu domin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar.

A jawabinsa, Malam Jamilu Maimasara, ya bayyana cewa kafa kungiyar ‘yan dako reshen karamar hukumar Dutse zai karfafi harkokin kasuwanci, inda ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagoranci domin samun nasarar aikin da ke gaban sa.

A nashi tsokacin, sabon shugaban kungiyar ‘yan dako reshen karamar hukumar Dutse Malam Abba Malamawa ya ce kofarsa a bude take don karbar shawarwari da kuma gyara, yayin da zai yi aiki da kowa da kowa domin cimma nasarar da ake bukata.

A nasa bangaren, Sarkin Dakon Dutse Malam Nasiru Manya, ya bayyana kafa reshen kungiyar a matsayin wani muhimmin ci gaba da ya samu sana’ar dako a karamar hukumar.

Kazalika, ya yi fatan hakan zai kawo karin cin moriya ga masu sana’ar dako da harkokin kasuwanci.

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara