Labarai
Mazauna Millennium City Sun Zargi Kaduna Electric Da Tilasta Sanya Masu Mita
Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba.
Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka.
Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo.
Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta.
Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin ya saka su cikin Band A — wanda aka fi warewa ga masana’antu da wuraren da ake amfani da wuta sosai — duk da cewa unguwanninsu wuraren zama ne na jama’a. Sun kuma bayyana cewa duk da ƙarin farashin, ba sa samun isasshen wuta da ya dace da tsarin Band A.
Wani daga cikin mazauna ya koka da cewa rashin tabbataccen wuta yana janyo musu asara, yana mai cewa: “Kayayyakinmu na lalacewa a cikin firiji, suna cewa muna kan Band A, amma a mafi yawan lokuta ba mu wuce awanni 15 da wuta a rana ba.”
Sai dai kamfanin Kaduna Electric ta bakin Mataimakin Daraktan Kamfanin, Abubakar Sadiq Mohammed, ya kare matakin da suka ɗauka, yana mai cewa ya yi daidai da ƙa’idojin hukumar NERC. Ya ce dokar ta tanadi cewa aƙalla kashi 40 cikin 100 na wutar da ake samu za ta tafi ga Band A, kuma ba abokin ciniki ke zaɓar irin band ɗinsa ba.
Ya ƙara da cewa shirin sanya mitocin kyauta yana cikin wani shiri ne da Bankin Duniya ke tallafawa domin kawar da tsarin ƙiyasta biyan kuɗin wuta da kuma samar da gaskiya a amfani da lantarki.
Lamarin ya ci gaba da jawo martani daga al’ummomin da abin ya shafa, inda ƙungiyoyin mazauna ke kira ga hukumomin da suka dace da su shiga tsakani domin tabbatar da adalci wajen tsarin mita da farashin wuta.
PR: Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
