Labarai
Matasan Kauru Sun Zargi Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin Tabuka Komai
Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken ‘Daga Fata zuwa Yaudara’ wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma ɗan siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al’umma.
Sanarwar ta koka da yadda al’ummar Kauru suka sanya kyakkyawan fata a shugabancin Danmaigona, amma a maimakon haka, ya kasa ba marada kunya.
Har ila yau, ta yi Allah-wadai da kawancen siyasarsa da Mukhtar Chawai, wani dan siyasa da aka ce ko ake zargin bai tabuka komai a mazabarsa ba, tare da bayyana cewa irin wannan kawancen yana kashe musu gwiwa matukar gaske.
KYA ta bayyana rashin jin dadin ta a kan abin da suka kira wasu ‘yan kudaden da basu gaza dubu 5 zuwa 10 da yake rabawa jama’a a matsayin yankawa kare ciyawa domin wannan ba abin da suke tsinanawa al’ummar da yake wakilta
Saboda haka Kungiyar ta bukaci al’ummar mazabar Kauru da su tashi tsaye akan nuna halin ko-in-kula a siyasance, su nemi wakilcin da ya dace, sannan su ki yarda a ba su kyauta irin wannan da bata tsinana musu komai.
Sun yi nuni da ‘yan majalisa irin su Hon. Shehu Yunusa na Kubau, wanda rahotanni suka ce ya ba da fifiko wajen hada kai da ci gaba, a matsayin misalan yadda wakilci na gaskiya ya kasance.
Da take kira da a wayar da kan ‘yan siyasa da kuma daukar matakin gama gari, sanarwar ta kalubalanci matasa da masu kada kuri’a a Kauru da su yi wa shugabanninsu hisabi, inda ta dage cewa zabe aiki ne..
KYA ta bayyana cewa Hon. Danmaigona ya samu damarsa, kuma har yanzu jama’a na nan suna jira, ba wai kawai alkawura ba, a’a, a samu canji na zahiri.
Rel/Yusuf Zubairu
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
-
Labarai2 days agoJihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki
-
Kasuwanci2 days agoBOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
-
Labarai5 days agoKashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya
-
Labarai2 days agoGwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida
-
Ilimi2 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
-
Labarai4 days agoGwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
