Labarai
APC Ta Yi Gangamin Karfafa Hadin Kan Mambobinta Bayan Kaddamar Da Aikin Titin Malam Madori
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.”
A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi.

Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori na nuna biyayya, karamci, da sadaukarwa wajen ci gaban jam’iyyar APC. “Wannan babbar shaida ce ta jajircewar Sanata Malam Madori ga jam’iyyarmu”.

Haka kuma Gwamnan ya karfafa gwiwar sauran mambobi da su tallafa wa shirin ci gaba na Shugaba Tinubu karkashin ‘Renewed Hope Agenda.”
Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya bayyana cewa tallafin motocin na nufin bai wa mambobin jam’iyya damar yin ingantaccen aiki wajen tallata shirin ci gaba na Shugaban kasa da kuma Shirin Ci Gaba na Gwamna Namadi.

“Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi sun kawo gagarumin ci gaba ga al’umma da ababen more rayuwa a Jigawa. An amince da kafa muhimman hukumomin tarayya, ciki har da Cibiyar Horar da ‘Yan Sanda a Kafin Hausa, Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Malam Madori, da Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma,” in ji shi.
Ya jaddada ayyukan Gwamna Namadi na baya-bayan nan, ciki har da aikin hanyar kilomita 47 da ke hada Hadejia–Garun Gabas, inganta asibitoci, da farfado da cibiyoyin lafiya na farko.

Sanata Malam Madori ya kara da jaddada hadin kan masu ruwa da tsaki na APC a mazabar Arewa maso gabashin Jigawa, wanda ya hada da ‘yan majalisar wakilai guda uku, ‘yan majalisar jihar guda tara, shugabannin kananan hukumomi takwas, da ‘yan majalisar kananan hukumomi 85
-
Ilimi7 days agoFarfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
-
Labarai3 days agoHukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
-
Ilimi3 days agoAn Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
-
Labarai5 days agoGwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
-
Labarai6 days agoAn Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita
-
Labarai6 days agoJigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
