Connect with us

Labarai

Mai Martaba Sarkin Kauru Ya Kara Ankarar Da Al’ummarsa Kan Matsalar Tsaro

Published

on

Mai martaba Sarkin Kauru a Jihar Kaduna, Alhaji Zakari Ya’u na biyu, ya kara  fadakar da al’ummar masarautarsa game da matsalar tsaro, duba da yadda ake  samun yawaitar satar mutane da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

 

Mai Martaba Alhaji Zakari Ya’u II, wanda ya bayyana haka a wajen taron buda baki na watan Ramadan na shekara-shekara a fadarsa da ke Kauru, ya jaddada muhimmancin yin taka tsantsan da hadin gwiwa da jami’an tsaro domin yakar kalubalen tsaro da ake fuskanta.

 

Mai Martaba Sarkin Kauru Alhaji Zakari Ya’u II

 

Sarkin ya kuma jaddada hakkin da ya rataya a wuyan ‘yan kasa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma, tare da yin kira da a hada kai domin tunkarar wadannan matsalolin yadda ya kamata.

Ya kuma nanata kiransa na ci gaba da hada kai da jami’an tsaro,  yana mai karfafa gwiwar mazauna yankin da su bayar da gudunmawarsu wajen inganta wayar da kan al’umma ta fuskar tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga kowa da kowa.

Alhaji Zakari Ya’u II, ya kuma jinjinawa daukacin wadanda suka halarci taron buda bakin na shekara shekara, yana mai nuna jin dadinsa bisa hakan, domin wata hanya ce ta sada zumunci a cikin watan Ramadan.

Da yake tsokaci game da mahimmancin taimako kuwa, Sarkin ya gabatar da wani hadisi da ke jaddada taimakon juna a tsakanin al’umma, inda ya bukaci jama’a da su kara jaiki wajen kara karfafa hakkin makwafta da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Hakazalika Martaba Alhaji Zakari Ya’u II, ya  yi addu’ar samun albarkar watan Ramadan ga dukkan mahalarta taron da iyalansu.

(Na tsakiya) Sakataren Majalisar Masarautar Kauru, Malam Muhammad Sani Suleiman (Dan buran Kauru)

 

A yayin taron, Sakataren Majalisar Masarautar, Malam Muhammad Sani Suleiman wanda shi ke rike da sarautar Dan Buran na Kauru, ya bayyana irin sadaukarwar da Sarkin yakeyi wajen tabbatar da jin dadin al’ummarsa da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautarsa.

 

Yusuf Zubairu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai16 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai17 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci2 days ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha2 days ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha2 days ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai2 days ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi5 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai7 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara