Connect with us

Labarai

BUKIN SALLAH: Sarkin Kauru Ya Nemi Al’umma Su Hada Kai Wajen Yakar Ta’addanci da ‘Yan Fashi

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kauru a Jihar Kaduna, Alhaji Zakariya Ya’u Usman II ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban domin yakar ta’addanci da ‘yan fashi a yankin.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin masu rike da mukaman gargajiya wadanda suka yi masa mubayi’a a fadarsa domin gudanar da bikin sallah babba na bana, inda ya jaddada cewa hadin kai da goyon bayan juna na da matukar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro da yankinsa ke fuskanta.

Mai Martaba Sarkin Alhaji Zakariyya Ya’u Usman ya bukaci al’umma da su hada kai, ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kiran na Sarkin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin shawo kan yawaitar munanan laifuka a yankin, wanda ke nuna irin rawar da hadin kan al’umma ke takawa wajen samar da yanayi mai tsaro.

Ya kara da cewa, a baya, tashe-tashen hankula da laifuka suna ta’allaka ne a kananan hukumomin da ke makwabtaka da su, amma a halin yanzu wadannan ayyuka sun mamaye yankin Kauru, lamarin da ke janyo hasarar rayuka da barnata dukiya, da kuma yin garkuwa da mutane.

Alhaji Zakari Ya’u II ya ce yayin da a hankali al’amura ke komawa ga al’ummomin da abin ya shafa, akwai bukatar ci gaba da kokarin yaki da rashin tsaro. Ya kuma ba da tabbacin cewa Gwamnati a dukkan matakai da Majalisar Masarautar Kauru suna aiki tukuru don ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula da aikata laifuka a yankin.

A cikin wata sanarwa da sakataren masarautar Kauru Malam Muhammad Sani Suleiman ya fitar, ya bukaci al’umma da su guji yada labaran da ba su da tushe balle makama ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta na zamani da sunan masarautar.

A cewarsa, duk wani bayani daga Masarautar dole ne ya bi ta hanyoyin da aka kafa kafin a yada shi ga jama’a.

Ya kuma jaddada mahimmancin sahihan bayanai da hadin kai a kokarin hadin gwiwa na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

COV/Yusuf Zubairu/Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara