Connect with us

Labarai

Kungiyar ‘Yan Sintiri Ta Bayyana Rashin Goyon Bayanta Kan Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

Published

on

Babban kwamandan Kungiyar ‘Yan sintiri ta Sakai ta kasa da aka fi sani da “Vigilante Group of Nigeria,” ya bayyana rashin goyon bayansu na kafa ‘Yansandan jihohi a Najeriya.

Babban kwamandan kungiyar Nebi Kaftin mai ritaya, Umar Bakori ya ce ba sa goyon bayan kafa Yansandan Jihohi a Najeriya, bayan da Kungiyar ta gabatar da gyare-gyare da ta ke so a yi a Kundin Tsarin Mulki ga kwamatin tsaro na Majalisar Wakilai a ranar Talatan nan.

Kaftin Bakori ya ce wannan yunkuri na kafa Yansandan Jihohi wata hanyace da ake amfani da ita wajen cinhanci da rashawa ta hanyar kwasar makudan kudade da sunan samar da tsaro.

Bakori ya ce Gwamnatin Taraiya ta kashe sama da Naira biliyan 13 don samar da Yansandan Al’umma amma hakan ya wuce babu wani canji da aka samu.

Ya bayar da misali da ikirarin Gwanonin Jihohin Katsina da Zamfara suka yi na cewa jihar Zamfarar ta kashe naira biliyan 10 kana jihar katsina ta kashe naira bilyan 17 domin samar da tsaro a jihohin su, sai dai acewarsa hakan bai samar da tsaron da a ke bukata ba a jihihin kawo yanzu

Ya ce Gwamnatin Jihar Ekiti ta kashe naira biliyan 1.4 da Jihar Ondo sun kashe naira biliyan 2 amma ba wata nasara.

In da ya ce a maimKon ha ka kamata ya yi gwamnonin su su tallafawa Kungiyar Vigilante don samar da tsaro a jihohin na su.

Kazalika ya kara da cewa tuni Kungiyar ta Vigilante na da mambobi sama da miliyan daya a Najeriya.

Kaftin Bakori ya ce mambobin su na da masaniya na wuraren da suke aiki kuma yan asalin yankin ne, sabo da haka suna da masaniya na lungu da sako na inda ma su laifi su ke, Sabo da haka suna taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri yadda ya da ce.

Ya ce Kungiyar ta su tana bukatar gwamnati ta amince da su kana ta basu kulawar da ta kamata ta hanyar basu tallafi na kudade a zama wani mataki na karfafa mu su gwiwa na cigaba da yin abun da suka sa kansu sama da shekaru 30 da suka gabata.

Shugaban ya bukaci Gwamnati ta samar da wata cibiya da za ta rinka bawa Yan Vigilante horo da Tsare-tsare da Dokoki don kyautata aikin su ta re da samar musu da kayan aiki da zai taimaka wajen samun nasarar aikin da su ke yi na rabbatar da tsaro a kasa.

Kwamandan ya nuna jin dadi na yadda Sojoji su ke basu hadin kai da goyon bayan ta yin aiki tare da juna, wanda hakan ya haifar da nasarori wajen kubutar da ‘Yan makarantar da aka yi garkuwa da su a Kuriga da Chibock da sauran wurare makamanta.

 

COV/Bashir M

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai13 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi15 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara