Labarai
Mai Martaba Sarkin Kauru Ya Kara Ankarar Da Al’ummarsa Kan Matsalar Tsaro
Mai martaba Sarkin Kauru a Jihar Kaduna, Alhaji Zakari Ya’u na biyu, ya kara fadakar da al’ummar masarautarsa game da matsalar tsaro, duba da yadda ake samun yawaitar satar mutane da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Mai Martaba Alhaji Zakari Ya’u II, wanda ya bayyana haka a wajen taron buda baki na watan Ramadan na shekara-shekara a fadarsa da ke Kauru, ya jaddada muhimmancin yin taka tsantsan da hadin gwiwa da jami’an tsaro domin yakar kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Mai Martaba Sarkin Kauru Alhaji Zakari Ya’u II
Sarkin ya kuma jaddada hakkin da ya rataya a wuyan ‘yan kasa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma, tare da yin kira da a hada kai domin tunkarar wadannan matsalolin yadda ya kamata.
Ya kuma nanata kiransa na ci gaba da hada kai da jami’an tsaro, yana mai karfafa gwiwar mazauna yankin da su bayar da gudunmawarsu wajen inganta wayar da kan al’umma ta fuskar tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga kowa da kowa.

Alhaji Zakari Ya’u II, ya kuma jinjinawa daukacin wadanda suka halarci taron buda bakin na shekara shekara, yana mai nuna jin dadinsa bisa hakan, domin wata hanya ce ta sada zumunci a cikin watan Ramadan.
Da yake tsokaci game da mahimmancin taimako kuwa, Sarkin ya gabatar da wani hadisi da ke jaddada taimakon juna a tsakanin al’umma, inda ya bukaci jama’a da su kara jaiki wajen kara karfafa hakkin makwafta da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Hakazalika Martaba Alhaji Zakari Ya’u II, ya yi addu’ar samun albarkar watan Ramadan ga dukkan mahalarta taron da iyalansu.

(Na tsakiya) Sakataren Majalisar Masarautar Kauru, Malam Muhammad Sani Suleiman (Dan buran Kauru)
A yayin taron, Sakataren Majalisar Masarautar, Malam Muhammad Sani Suleiman wanda shi ke rike da sarautar Dan Buran na Kauru, ya bayyana irin sadaukarwar da Sarkin yakeyi wajen tabbatar da jin dadin al’ummarsa da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautarsa.
Yusuf Zubairu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari



