Connect with us

Fasaha

Tarihi Da Darussa 7 Daga Yaƙin Badar Da Aka Gwabza Ranar 17, Ga Ramadan

Published

on

Yaƙin Badar ya faru ne a 17 ga watan Ramadan a shekara ta biyu bayan hijira, shi ne na farko tsakanin ƙuraishawa da Annabi (SAW), wanda a ƙarshe Allah ya bai wa Annabi (SAW) da sahabbansa nasara, a sanadiyyar abubuwan da suka wakana a yaƙin da irin sakamakon da ya haifar ya zama shi ne yaƙi mafi girma da falala a musulunci, sahabban da kuma suka halarci yakin suka zama na musamman.

Wannan yaƙin yana ɗauke da dimbin darussa wanda da al’umma za ta kiyaye su to ba ƙaramar nasara za ta cimma ba, kaɗan daga cikin waɗannan darussa akwai:

1- Muhimmancin Tsari Da Kyakkyawar Gudanarwa:

•”Taron marasa lafiya ba ya samar da ƙarfi sai dai ya samar da asibiti” [Al-Mu’utamid bin Abbad].

A tsakanin bangarorin guda biyu, ɓangaren Musulmai shi ne mafi ranuni ta fuskar yawa da kuma kayan yaƙin, domin daman can ba da niyyar yaƙin farko suka fito ba, amma a sakamakon kyakkyawan tsari na Annabi (SAW) da iya gudanarwa tun daga kan gaggauta fara isowa wurin da za a fafata (Badar), da zaɓar mafi dacewar wurin kafa sansani da kuma tsara su kansu mayakan da sauran abubuwa, musulmai suka iya cin nasara tare da cewa waɗnada suke yaƙa ɗin kafiran makka sun fi su yawa da kayan aiki da shirin yaƙin, wanda wannan yana nuna cewa ƙarancin abun hannu ko arziki ba ya hana cin nasara da samun ci gaba matuƙar al’umma ko ƙasa ko gwamnati tana da kyakkywan tsari da kuma iya gudanarwa, hakanan yawa da wadata ba ya bayar da nasara matuƙar al’umma ko ƙasa ko gwmanti ta kasance a hargiste ko lalaltaciyya ba ta tsari ba, domin taron marasa lafiya baya haɗa ƙarfi sai dai ya haɗa asibiti.

2- Muhimmancin Shawara:

•”Jama’a ta yi kuskure ya fi mutum ɗaya ya yi daidai domin in ya iya cankar daidai sau ɗaya to ya yi ta faɗawa kuskure sau da yawa, kuma ya rasa wanda zai mai uzuri” [Ibrahim Al’andalusy].

Shawara ta taka muhimiyyar rawa a nasarar Musulmai a wannan yaƙi, Annabi (SAW) duk da cewa shi ya fi kowa hankali da tinani da hangen nesa bugu da ƙarima ana saukar masa da wahayi amma duk da haka sai da Allah ya umarce shi da ya dinga shawara har abu Huraira yake cewa: banga wani mai yawaita neman shawarar sahabbansa ba sama da Manzon Allah (SAW) ba. Wanda wannan yake nuna muhimmancin shawara kuma babu wanda yake wadatuwa daga gareta komai irin iliminsa da wayewarsa da kaifin tunaninsa, hakanan shawara ita ce mabuɗin ci gaba da nasar al’umma da ita ne ake iya haɗa kan al’umma domin duk wanda ya ga ana yi da shi to wannan zai ƙara masa dangantuwa zuwa ga al’ummarsa, zai ba ta gudunmowa sosai domin yana jin cewa al’ummarsa ce ba ta wani ba, hakanan da shawara ne a kan iya naɗa wanda ya dace a idan ya dace, da kuma shawara ne ake iya kubuta daga faɗawa hatsarin ringingimu da faɗace-faɗace, don haka wajibi ne a ɗabbaƙa shawara kuma a neme ta a wurin kowa domin iya aiwatar da shawarar, iya nasarar da za a cimma ko da kuwa wannan al’umma musulma ce ko kafira.

3- Dagewa Da Addu’a Da Kuma Dogaro Da Allah:

•”Watakila nasara tana jinkiri saboda al’umma ta ƙara ƙarfin alaƙarta da Allah a yayin da take fama take shan wahala, sai ta ga ba ta da wani sai Allah. Hakan sai ya sa ta dawo kan turba da gawadabe na gaskiya, kuma idan ta samu nasara hakan ba zai sa ta karkace daga kan hanyar gaskiya da alheri da adalci ba, don ta san da su ne Allah ya bata nasara.” [ Sayyid Qudub].

Duk da cewa Annabi (SAW) ya san shi da sahabbansa su ne a kan gaskiya, kuma Allah ma ya yi mai alƙawarin nasara amma bai shantake ba, bai ce “Cin Nasara Dole” ba duk bai yi hakanan ba sai dai dagewa da dogewa a kan addu’a har sahabbansa, sannan suka fara ganin kamar abun ya yi yawa, wanda a sanadiyyar haka Allah ya saukar masa da nasararsa.

Anan zamu fahimci cewa Dogaro da Allah da kuma yin addu’a shi ne babban makamin nasara bayan mutum ya gama ɗaukar dukkanin matakai.

Rashin riko da wannan jigo yana jawowa a gagara samun nasara a rayuwa, domin ƙarfin musulmi daga Allah yake nasarar kuma ta shi ce, shi yake bayar da ita ga wanda ya ga dama, shi yasa a ko wane hali Annabi (SAW) yake ba ya ƙin addu’a, ba ya ƙin saka Allah a lamarinsa, bal kodayaushe yana ƙara nasara da ɗaukaka, yana ƙara ta’allaka da Allah.

4- Jagoranci Shi ne Ginshikin Al’ummah:

•”Idan kana son kassara ko wacce al’umma, to ka fara gusar da jagororinta ko mayar da su ƙarƙashinka”

A yaƙin Badar an kashe kafirai 70, a yaƙin Uhud kuma an kashe muslmai 70 amma a yaƙin Badar aka yanke cewa musulmai sun yi nasara a kan kafirai saɓanin yaƙin Uhud wanda duk da an yi wa musulmai ɓarna amma kuma ba a ci nasara a kansu ba, me ya bambanta waɗannan yaƙe-yaƙen biyu? Abin da ya bambanta su shi ne jagorori, kafiran Makkah sun yi asarar jagororinsu da yawa a Badar, wanda rashinsu ne yasa daular Makkah ta fara shiga rauni har aka cinyeta a ‘Fathu Makkah,’ sabanin yaƙin Uhud wanda muslmai ba su yi wannan asarar ba shi yasa ma har Abu Sufyan ya shiga tambaya ko an kashe Annabi (SAW) da Abubakar da Umar? Saboda ya san a cikin kashe waɗannan nasarar gaske take samuwa, daganan kafiran suka sake cin alwashin sai an sake haɗuwa a Badar sun ɗau fansa duk da irin barnar da suka yi uhud amma hakan bai gamsar da su ba.

Jagorori su ne ƙashin bayan kowacce al’umma, duk sanda aka yi niyyar kassara wata al’umma ko tafiya ana farawa ne daga kan jagorinta ko dai a kawar da su, ko kuma a shigar da su ƙarkashin wani ikon ta yadda za a dinga juya wannan al’umma ko tafiya yadda ake so, don haka in kana son auna lafiyar al’umma ko tafiya to ka duba jagorancinta.

5- Sadaukarwar Sahabbai:

•”Na je wurin Qaisar da Kisra da Najashi, amma banga wanda mutanesa suke girmama shi ba, suke son shi ba kamar yadda Sahabban Muhammad (SAW) Suke girmama Muhammad (SAW) ba” [Urwa bin Mas’ud Assaqafy].

A wannan yaƙin zamu ƙara gane cewa lallai sahabban Annabi (SAW) zaɓaɓɓu ne daga Allah, za mu ga yadda imani ya gama mamaye zukatansu ta yadda tun farko suka yadda suka marawa Annabi (SAW) baya a wannan yaƙin da duk wasu ma’aunan ɗan adam suna nuni da cewa ba yadda za a yi a ci nasara, amma haka suka yadda suka ƙutsa cikin halaka ba tare da la’akari da wannan ba, suna masu yaƙar iyayensu da ƴan uwansu da ƴan danginsu ba don komai ba sai don ƙasancewar imani sama yake da komai a wurinsu, sama yake da ƴan uwantaka sama yake da ƙasa, da wannan imanin da sadaukarwar ne sahabbai suka kai matsayin da suka kai.

6- Cikakken Kishi Da Soyayya Yana Ga Addinin Allah Ne:

“Da a ce a kan ƴan uwantaka ko ƙabila ko ƙasa ake kulla soyayya ko ƙiyayya da Annabi (SAW) bai barranta daga baffansa Abu-Lahab ba yaƙi Ƙuraishawa ba, da kuma barin makkah ba sai ana gina wala’ine a kan aƙida wadda tafi jini da ƙasa tsada” [ Adham Assharqawy].

A wannan yaƙin za mu ga yadda Annabi saw da sahabbansa suka yi yaƙin ƴan uwansu ƴan ƙabilarsu ƴan garinsu wanda a ma’aunin wannan zamanin hakan cin amanar ƙasa ne da rashin kishinta. A nan za mu ga cewa a musulunci babu wata alaƙa da take sama da ta addini a kansa ne musulmi yake ƙulla soyayya yake kuma kulla ƙiyayya ba tare da la’akari da ƙasa ko launi ko jinsi ba, hakanan a musulunci babu wani abu da ake kira da kishin ƙasa a ma’anarsa ta yau, kasar musulmai ita ce in da yake samun ƴancin bautar Allah ba in da Turawa suka zana a takarda ba.

7- Izzar Al’umma Tana Cikin Aiwatar Da Jihadi:

•”Jihadi yana kare al’ummah ta sanadiyyarsa ya kuma sake dunƙulewa, barinsa kuma shi yake kacaccalata ya ɗaiɗaitata” [ Abdul’Aziz Attarify].

Sakamakon yaƙin Badar Muslmai sun zama wani ƙarfi da kowa yake tsoron tinkara, ya sanya musu kwarjini a idon abokan gaba, ya kuma ɗaukaka su. Wannan shi yake ƙara nuna mana cewa lallai izzar al’umma da ɗaukakarta tana cikin aiwatar da jihadi, rashin aiwatar da shi shi zai kaita zuwa ga ƙasƙanci da halaka, kamar yadda muke gani a yau, yana daga cikin alfanun jihadi kawar da saɓani da haɗe kan al’umma domin tunkarar babban abokin gaba, hakanan da jihadi ne al’umma take ƙara samun kwanciyar hankali da yalwa da arziki shi yasa duk wanda ya karanta tarihin musulmai zai ga cewa babu sanda suka fi samun aminci da wadata sai a lokutan jihadi, babu sanda suka shiga ƙaskanci da rashin tsaro da talauci sai sanda suka saki jihadi, wanda daman wannan shi ne alƙwarin Allah.

Don haka duk da cewa yanzu ba aiwatar da jihadi ba, idan dai ba a inda suke fuskantar yaƙi ba, amma wajibi ne a sanar da al’umma, shi ya zamanto a ƙwaƙwalenta ko da ba ta da halin aiwatar da shi.

Waɗannan wasu darussane da zamu iya amfana daga yaƙin Badar. Allah ya datar da mu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai14 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi16 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara