Kasuwanci
Gwamna Sule Yayi Murnar Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Najeriya
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai.
Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa.
Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da marawa kyawawan manufofi da shirye-shiryen wannan gwamnati goyon baya.
Sannan ta bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa da hadin kai da lumana ba tare da la’akari da bambancin addini, kabilanci da siyasa ba.
Daga nan sai sanarwar ta yi jinjina ga sadaukarwar da jaruman da suka gabata suka yi, ta kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa kasan nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Rel/Aliyu Muraki/Lafia.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
