Labarai
Hisbah Ta Kama Wani Mutum Da Ke Yunkurin Safarar Mata 12 A Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da safarar mutane tare da mata 12 a wata tashar mora da ke kan titin Zaria.
Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne yana yunkurin safarar matan zuwa Legas.
Mataimakin Kwamandan Janar na Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya ce jami’an hukumar karkashin jagorancin jami’in da ke kula da tashoshin mota, Muhammad Bashir ne suka cafke wanda ake zargin, wanda dan asalin jihar Borno ne.
Bincike na farko ya nuna cewa an shirya safarar matan ne zuwa kasashen waje ta hanyar Legas, inda za su bi ta Jamhuriyar Benin da kumGhana, sannan daga bisani a kaisu Saliyo.
Ana zargin wanda aka kama da tsara musu takardun izinin shiga kasar Saudiyya domin neman aikin yi.
A cewar Hisbah, matan sun bayyana yayin bincike cewa kowannensu ta riga ta biya Naira miliyan ɗaya da rabi (₦1.5m) a matsayin kafin alkalami, tare da yarjejeniyar cewa za su biya sauran kudin bayan sun samu ayyukan yi a ƙasar da za a kaisu.
Hukumar ta nuna damuwa cewa irin wannan kudi mai yawa na iya zama jari domin dogaro da kai a gida.
Aminuddeen ya ce matan sun bambanta a shekaru, ciki har da wadda ta kai shekara 50, wasu biyu ’yan shekara 23, wasu biyu kuma ’yan shekara 20, yayin da sauran mafi yawan su ’yan shekara 15 ne kacal. Sun fito ne daga jihohin Katsina, Kano, Borno, Jigawa da Zamfara.
“Wannan abin takaici ne,” in ji shi. “Kudin da suka biya ya isa su fara sana’a mai kyau a jiharsu. Amma suka zabi su sa kansu cikin hadarin irin wannan tafiya.” Ya bukaci iyaye da su ja hankalin ’yayansu game da irin waɗannan lamurra masu hadari.
Kwamandan ya gargadi cewa ko da sun samu takardar izinin shiga Saudiyya, babu tabbacin aikin da za su yi a can. “Idan kuma an kasa samun visa, za a karkatar da su zuwa Saliyo. Wannan lamari hadari ne kuma abin takaici,” In ji shi.
Daga karshe, hukumar Hisbah ta mika wanda ake zargi da matan ga Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) domin gudanar da cikakken bincike da daukar matakan da suka dace.
Daga Khadijah Aliyu
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
