Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoma 352 A Nasarawa Da Kayayyakin Noma Na Zamani

Published

on

Gwamnatin Tarayya tare da Asusun Samar da Kudade Domin Bunkasa Harkokin Noma(IFAD) da Shirin Sarrafa Amfanin Gona (VCDP) sun fara raba kayayyakin noman zamani da mashin mai kafa uku  ga manoma 352 a Jihar Nasarawa domin kakar noman bana.

Shugabar shirin IFAD-VCDP, Dr. Eunice Adgidzi ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a Lafiya, babban birnin jihar, inda ta ta bayyana cewa shirin ya fi karkata ne ga kanana manoman shinkafa da rogo.

Ta ce shirin wani bangare ne na ƙoƙarin da ake yi na sauya fannin noma zuwa abin da zai kawo wadatar abinci, samar da arziki da kuma ci gaba mai ɗorewa a Jihar Nasarawa.

Manoma 352 da suka amfana an zaɓo su ne daga kananan hukumomi biyar da shirin ya shafa a jihar, da suka hada da Lafiya, Nasarawa, Doma, Karu da Wamba.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan iri shinkafa mai  nauyin kilo 9,600, da buhunan 1,408 takin NPK 1,408, da buhuna 384 na takin Urea, da lita 352 na maganin ciyawa mara zaɓi, da lita 352 na maganin ciyawa mai zaɓi, da kuma rassa 8,000 na rogo domin dashe.

Haka kuma, an raba mashin mai kafa uku guda tara ga wasu manoma domin sauƙaƙe musu jigilar kayan gona zuwa kasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen rage asarar bayan girbi.

Dr. Adgidzi ta jaddada cewa haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da IFAD da gwamnatin jihar, na nuna jajircewar samar wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu wajen samun nasara.

A nasa jawabin, Kwamishinan Noma na Jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Tunga, ya bayyana cewa wannan shiri zai ƙara samar da abinci, rage asarar bayan girbi da kuma inganta rayuwar kananan manoma.

Ya shawarci manoman da suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, sannan ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa samar da yanayin da ya ba da damar nasarar shirye-shiryen noman a jihar.

A martanin su, wasu daga cikin manoman da suka amfana kamar su Lazarus Okwugya daga Assakio, da Joseph Abimiku da Fatima Shuaibu daga unguwar Azuba, sun nuna godiya ga shirin VCDP bisa irin tallafin da ya kawo, wanda suka ce ya inganta yawan amfanin gona da kuma rayuwarsu.

 

Daga Aliyu Muraki

 

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara