Ilimi
Malaman Jami’ar Kwara Sun Yi Zanga-Zangar Lumana
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kwara da ke Malete (KWASU), ta gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Laraba domin neman a biya su kudaden alawus-alawus na EAA da sauran hakkokinsu.
Malaman a karkashin inuwar ASUU sun ce sun shiga sahun sauran rassan kungiyar a fadin ƙasa wajen matsa lamba kan gwamnatin tarayya da ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da ASUU tun shekarar 2009.
Shugaban ASUU reshen KWASU, ya bayyana cewa jinkirin biyan EAA da sauran hakkoki ya sanya malamai cikin mawuyacin hali, inda da yawa daga cikinsu ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Ya ce duk da ƙalubalen da suke fuskanta, malamai na ci gaba da gudanar da ayyukansu na koyarwa da bincike, sai dai yanzu tura ta kai bango.
“Mun fito ne domin nuna damuwarmu da kuma jawo hankalin gwamnati. Babu shakka, ci gaban ilimi ba zai yiwu ba idan malamai ba su samu kulawa da gata ba,” In ji shi.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Kwara da ya yi wajen ganin an warware matsalar cikin gaggawa.
ASUU ta yi gargadin cewa, idan aka ci gaba da watsi da bukatunsu, ba za su yi jinkiri ba wajen ɗaukar matakan da suka fi wannan tsauri a nan gaba.
Ta yi kira ga ɗalibai, iyaye da sauran jama’a da su fahimci matsayin da suke ciki, tare da goya musu baya wajen kare martabar ilimi da neman hakkinsu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
