Ilimi
AMA Foundation Da FGC Kaduna Sun Hada Kai Domin Tallafawa Ilimin Marayu A Jihar Kaduna
Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna.
Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare na Gwamnatin Tarayya kai tsaye.
Yayin taron Annual Speech and Prize-Giving Ceremony na makarantar, Shugaban makarantar Hauwa’u Memorial, Nasir Musa, wanda ya wakilci AMA Foundation, ya bayyana cewa yanzu haka ana daukar nauyin marayu 120 a makarantar firamare, wasu 120 a Makarantar Sakandare na FGC Kaduna, sannan dalibai 16 sun samu gurbin shiga Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Ya jinjina wa wanda ya assasa wannan makarantara Alhaji Musa Bello, saboda kafa wannan gagarumin aikin da ke mayar da hankali wajen kula da marayu, yana mai cewa hakan zai basu damar cika burinsu.
Babban malamin makarantar FGC Kaduna, Prince Adewale Adeyanju, shi ma ya yaba wa AMA Foundation saboda daukar nauyin karatun marayu daga firamare har jami’a, yana mai bayyana shi a matsayin kyawawan abubuwan da mutum zai iya bayarwa ga al’umma.
Ya bayyana cewa dukkan daliban da aka dauki nauyi a wannan shekara sun kammala da sakamako mai kyau, wanda zai ba su damar samun gurbi a manyan jami’o’i a duniya.
A nashi jawabin, a madadin Shugabar Asibitin Ido na Tarayya dake Kaduna, Dr. Amina Hassan, Dr. Sadiq Muhammad ya bayyana gamsuwarsa da irin ilimin da aka ba wa wadannan marayun.
Ya kuma yi kira ga sauran masu hali su yi koyi da wannan irin wannan kyautatawa.
Shugaban Daliban Maza wato Head Boy, Ibrahim Usman Waziri, da ta bangaren mata, Hafsat Adam Waziri, sun nuna farin cikinsu da kasancewa cikin daliban da suka kammala.
Sun yi kira ga iyaye su tabbatar da ganin ‘ya’yansu sun samu ilimin addinin Musulunci da na zamani tare.
Iyaye da ‘yan uwa na wasu daga cikin daliban da suka kammala, ciki har da Asmau Ahmed da Sabi Yusuf (uwa da kawu), sun gode wa AMA Foundation saboda damar da ta ba ‘ya’yansu wajen canza rayuwarsu.
A yayin bikin kaddamar da littafi da aka gudanar a wajen taron, Babban Daraktar na AMA Foundation, Aisha Yusuf Mamman, wacce ba ta samu halarta ba ta aiko da sakon fatan alheri, yayin da Mataimakiyar Babban Darakta, Fatima Bala Jafar, ta bada gudunmawar naira ₦50,000.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
