Connect with us

Kasuwanci

Za A Sabunta Filin Jiragen Sama Na Ilori Zuwa Cibiyar Jigilar Kayayyaki Ta Zamani

Published

on

Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci.

Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da Hukumar FAAN ta shirya domin sanar da shirin fara jigilar kayayyaki a Filin Jiragen Sama na Ƙasa da Ƙasa na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilori.

A cewarsa, wannan shiri na nufin kara inganta matsayin jihar tare da ƙarfafa rawar da take takawa a harkokin kasuwanci na cikin gida da waje.

Ya jaddada cewa aikin ya yi daidai da manufofin wannan gwamnati na buɗe sababbin hanyoyin fitar da kayayyaki, bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga ga masu samar da kayayyaki da  ‘yan kasuwa.

Dakta Abolore ya ce jigilar kayayyakin ta jiragen zai sauƙaƙa daukarsu daga gonaki, zuwa masana’antu, da wuraren sana’o’i zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, wanda hakan zai  ƙara musu daraja, sarrafawa da a fannoni daban-daban.

Kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai rage asara, ya kiyaye ingancin kayayyaki, sannan ya bunƙasa damar kasuwanci a fannin kayayyakin gona, masana’antu, da kayayyakin da aka sarrafa.

Ya nuna cewa saboda cunkoson da ake samu a tashoshin jiragen sama da na ruwa da ke  Legas, garin Ilori na wata dama ta musamman wajen samun fitar da kayayyaki cikin lokaci da inganci, tare da ƙara wa jihar damar gogayya da jihohi da ma kasashen duniya.

Dakta Abolore ya yi kira ga manoma, ƙungiyoyi, masu masana’antu, masu saka jari, ƙungiyoyin sufuri, ‘yan kasuwa, masu sarrafawa, da hukumomin da ke kula da doka da tsari, da su haɗa kai wajen kara inganci, yadda ake shirya kayayyaki daidai da zamani, da amfani da fasaha domin bin ka’idojin kasuwannin ƙasashen waje.

Shi ma Manajan Filin Jirgin Sama na Janar Tunde Idiagbon, Mista Suraju Aderibigbe, ya bayyana cewa za a sabunta tsohon ginin tashar zuwa sabuwar cibiyar jigilar kaya mai amfani da fasahohi na zamani domin tabbatar da tsaro wajen sarrafa nau’ukan kayayyaki daban-daban.

Ya tabbatar da cewa wannan gyara zai ƙara bunƙasa kasuwanci, samar da ayyukan yi, da kuma ci gaban tattalin arziki a fannoni da dama a jihar.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara