Labarai
Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kukah Centre ta ce ta kuduri aniyar horar da jami’an tsaro a jihohin Sokoto, Kaduna da Benue.
Daraktan Cibiyar Kukah Reverend Father Atta Barkindo, wanda ya bayyana hakan ya ce an dauki matakin ne domin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar al’ummar kasar.
Reverend Father Atta Barkindo, ya jaddada cewa an shirya horon ne domin inganta tsaro a tsakanin al’umma a cikin dimbin kalubalen da jihohi da dama ke fama da su a fadin kasar nan.
Ya kuma bayyana bukatar kafa jami’an tsaro na Jihohi su samar da ingantattun tsare-tsare don tabbatar da samar da ayyuka masu inganci.
Shima da yake jawabi, jami’in kula da ayyukan cibiyar Kukah, Terseer Bamber, ya yi nuni da cewa, wasu daga cikin jami’an tsaron jihar sun fuskanci tuhume-tuhume na take hakkin dan Adam da cin zarafin mata.
Ya jaddada mahimmancin magance wadannan matsalolin a matsayin wani abin da ake bukata domin samun ci gaba mai dorewa a Najeriya.
Ana aiwatar da aikin horon ne tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kukah, Ci gaban Ƙasashen Duniya na Birtaniya, da Tetra Tech International Development.
A nasa jawabin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar wanda Sarkin Yakin Gagi, Hakimin Gagi Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yi maraba da shirin inda ya bayyana cewa Sarkin Musulmi a shirye yake ya tallafa wa duk wani kokari da zai taimaka kai tsaye wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
Ya bukaci gwamnatocin jihohi da su ba da fifiko wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai, yana mai korafin cewa kalubalen tsaro ya yi matukar tasiri ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Rediyon Najeriya ya rawaito cewa taron ya samu halartar wakilai daga jami’an ‘yan sanda, da Civil Defence, masu aikin shari’a, ‘yan majalisar dokoki, da kuma shugabannin gargajiya, inda ya bayyana tsarin hadin gwiwa na inganta tsaro a Najeriya.
Nasir Malali/Sakkwato
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
