Kasuwanci
NEPC Ta Horas da Mata Kan Damar Kasuwancin Fitar da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Ƙarfafa Fitar da Kayayyaki ta Ƙasa (NEPC), reshen Jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta fara taron wayar da kan mata na tsawon kwanaki biyu kan damar kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje a ranar Asabar.
Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Shugaban ofishin kula da Jigawa, Alhaji Abdulkadir Aliyu, ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan mata ’yan kasuwa game da damar shiga kasuwannin duniya.

A cewarsa, manufar taron ita ce samar da ƙwararrun mata masu fitar da kayayyaki, tare da basu damar samun tallafin kasuwanci, hanyoyin sadarwar kasuwanci, da damar samun kuɗaɗen jari.
Ya ce “Tsawon kwanaki biyun nan, muna fatan ƙarfafa shigar mata cikin kasuwanci ta yanar gizo, da fitar da kayayyaki masu ƙarin daraja”.

“Wannan taron zai ƙarfafa mata, bunƙasa tattalin arzikinmu na cikin gida, da faɗaɗa hangen nesan kasuwancin da mata ke mallaka da jagoranta a jiharmu“.
Alhaji Abdulkadir Aliyu ya ƙara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar na bunƙasa tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa, tare da tallafa wa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa (MSMEs) da kuma shigar mata cikin harkokin tattalin arziki.

A jawabinta, wata mai aikin sa-kai Hauwa Isa Muhammad daga ƙungiyar agaji mai zaman kanta ta ImpactHer, ta ce suna haɗin gwiwa da NEPC wajen gudanar da taron wayar da kai domin ba mata ƙwarewar tallata kasuwanci ta hanyar kafafen zamani .
A cewarta, suna jihar Jigawa ne domin tallafa wa mata ’yan kasuwa 30 wajen sauya kasuwancinsu zuwa tsarin fasahar zamani , domin samun damar shiga kasuwannin duniya.

Ta ce“A matsayin wani ɓangare na tallafinmu, muna bayar da tallafin kuɗi dala 500 ga mahalarta biyu da suka nuna ƙwazo da niyyar haɓaka kasuwancinsu zuwa matakin duniya.”
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Jihar Jigawa, Alhaji Mukhtar Birniwa, ya yabawa ƙoƙarin NEPC da ImpactHer bisa tallafin da suke bai wa matan Jigawa.

Birniwa ya jaddada cewa da irin wannan tallafi, matan Jigawa za su bunƙasa tattalin arzikinsu da na ƙasa baki ɗaya, tare da sadasu ga kasuwannin duniya.
Ya kuma sake tabbatar da kudirin ƙungiyar na yin haɗin gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa ƙwarewar mata gaba ɗaya.
Da take magana a madadin mahalarta taron, Hauwa Umar ta yabawa NEPC da ImpactHer bisa sabbin ƙwarewar da suka samu.
Ta ce za su yi hulɗa da sauran ƙungiyoyin mata da ba su samu damar halartar taron ba domin su amfana da abin da suka koya.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa ofishin NEPC na Jigawa ya shirya taron wayar da kan mata ’yan kasuwa na tsawon kwanaki biyu a ranar Asabar 13 da Lahadi 14 ga watan Disamban 2025.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
