Labarai
An Fara Gyaran Tashar Talabijin Ta Jigawa Don Kara Mata Nisan Zango
Gidan Talbijin na Jihar Jigawa wato JTV, ya fara gudanar da gyare-gyaren doguwar eriyar yada shirye-shiryen tashar dake garin Andaza.
Da yake yiwa shugaban gidan Talabijin na JTV Alhaji Abba Tukur karin bayani kan fara aikin, jagoran tawagar injiniyoyin, Injiniya Obi Onya, ya ce za su gudanar da aikin ta hanyar gano sassan doguwar eriyar da suke da matsala.

Injiniya Onya ya bayyana cewar, haka kuma za su gudanar da irin wannan aikin a kananan tashoshin yada shirye-shiryen tashar dake garuruwa 3 na kananan hukumomi a Jihar.

Yana mai cewar, garuruwan su ne Gumel da Hadejia da kuma Kazaure.


Shugaban gidan talabijin din wanda ya sami wakilcin Manajan Sashin injiniya na JTV, Malam Sha’aban Abubakar Tahir, ya yi bayani kan muhimmancin yi wa doguwar eriyar gyara, wanda ya ce zai karawa tashar nisan zango.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
