Labarai
Sabon Tsarin Sufuri Na BRT Zai Rage Kudin Sufuri Da Zirga-Zirga A Kaduna
Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi.
Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kada Hive da ke Kaduna.
An shirya taron ne domin wayar da kan jama’a game da shirin BRT, sannan matakan da aka dauka ya zuwa yanzu.
Taron an gudanar da shi ne domin sauraron ra’ayoyin al’umma kan yadda za a aiwatar da shi cikin nasara.
Injiniya Inuwa ya bayyana cewa tsarin BRT zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da kara tsaro da aminci, da kuma inganta rayuwar al’umma baki daya a Jihar Kaduna.
Ya tuna cewa kimanin watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Uba Sani ya kaddamar da sama da motoci 100 masu amfani da iskar gas na CNG, wadanda za su rika zirga-zirga a cikin Birnin Kaduna, Zariya da Kafanchan, a wani bangare na kokarin gyara tsarin sufuri a fadin jihar.
Ya bukaci mahalarta taron su yada ilimin da suka samu zuwa cikin al’ummominsu domin kara fahimta da goyon bayan jama’a don nasarar wannan shiri.
A nasa bangaren, Ted Regino, shugaban Rebel Artic Joint Venture, wanda ke sa ido kan kwangilolin aikin, ya ce kamfaninsa ne ke lura da yadda ake gudanar da aikin.
Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin BRT kafin shekarar 2027, tare da karin bayani cewa kamfaninsu ya taba aiwatar da manyan ayyuka a kasa da kasa, kuma hakan zai maimaitu a Jihar Kaduna.
A nata jawabin, Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa, Hajiya Rabi Saulawa, ta yaba da wannan shiri, tana mai cewa zai rage wa mata wahalhalun sufuri, musamman wadanda ke yawan zirga-zirga zuwa asibitoci, kasuwanni, wuraren aiki da makarantu.
Wasu daga cikin mahalarta sun jaddada bukatar kulawa da kiyaye motocin, tabbatar da dorewar shirin, da kuma kawo karshen matsalar sayar da tikiti ba bisa ka’ida ba.
Taron ya samu halartar wakilai daga sashen sufuri, shugabannin addinai da na gargajiya, ’yan jarida da sauransu.
COV: Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
