Connect with us

Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Samu Goyon Bayan Mazauna Mahuta Bayan Warware Rikicin Filaye

Published

on

 

Mazauna unguwar da asibitin kula da ido ta kasa yake wato Mahuta da ke jihar Kaduna sun amince da Gwamna Uba Sani ya zarce karo na biyu, biyo bayan warware takaddamar filaye da aka dade ana yi wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje da dama a gwamnatin da ta gabata.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta hannun hukumar kula da bayanan kasa ta jihar Kaduna (KADGIS) ta bayar da shedar mallakar filayen sama da 300 ga al’ummar da rusau da aka yi a zamanin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya shafa.

Da yake jawabi a madadin mazauna yankin, Kanar Haruna Idris Zaria mai ritaya, ya yabawa Gwamna Sani bisa abin da ya bayyana a matsayin tsarin sa na tausayi da kishin al’umma.

Ya ce matakin da gwamnan ya dauka cikin gaggawa da tsari ba kawai ya kawo karshen rashin tabbas na tsawon shekaru ba har ma ya dawo da kwarin gwiwar mazauna yankin ga gwamnati.

“Mun sha wahala na tsawon shekaru, ba tare da sanin ko gidajenmu za su taba zama namu ba, amma Gwamna Uba Sani ya ba mu goyon bayan doka da kwanciyar hankali, abin da ya yi ya nuna shugaba mai saurare da tausayawa,” in ji Zaria.

Mazauna yankin sun ce bayar da takardun mallakar filaye ya rage tashe-tashen hankula a tsakanin al’ummar Mahuta, inda aka dade ana jira a tabbatar da mallakar kadarorin.

Mazauna yankin sun ce bayar da takardun mallakar filaye ya rage tashe-tashen hankula a tsakanin al’ummar Mahuta, inda aka dade ana jira a tabbatar da mallakar kadarorin.

Har ila yau, sun yaba wa Gwamna Sani da ya dakatar da duk wani rusau na gidaje, inda ya baiwa iyalai damar rayuwa ba tare da fargabar gudun hijira ba.

“Wannan ya wuce nasara ta doka, na jin kai ne,” in ji wani mazaunin.

“Gwamnan ya dawo mana da mutunci da kwanciyar hankali a rayuwarmu.”

An yaba da yadda Gwamna Sani ya tafiyar da rikicin filaye na Mahuta a matsayin abin koyi wajen magance rikicin filaye a birane.

An bayyana shirin a matsayin shaida na yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da adalci, gudanar da mulki tare da kare hakkin talakawan kasa.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa, wannan goyon bayan da aka samu daga tushe na iya karawa Gwamna Sani karfin guiwa a siyasance gabanin zabe mai zuwa, musamman idan aka yi la’akari da yadda al’amuran mallakar filaye ke damun garuruwan Kaduna.

Ga mazauna Mahuta kuwa, amincewar su ya samo asali ne daga godiya ba siyasa ba.

“Ya sami amanarmu ta hanyar yin abin da wasu ba za su yi ba,” in ji Kanar Zaria.

“Mun yi imanin ya cancanci wa’adi na biyu don ci gaba da kyakkyawan aiki,” in ji masu lura da al’amuran.

Umar S Fada

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara