Connect with us

Fasaha

Ana Kaddamar Da Sabbin Ajujuwa A Makarantun Jihar Kaduna

Published

on

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya kaddamar da azuzuwa 24 a babbar makarantar firamare karo na biyu a jihar, tare da daukar dalibai sama da dubu bakwai a makarantar firamare ta Rafin Guza da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

 

A Lokacin da Gwamnan ke kaddamar da azuzuwan ya ce kowa ya shaida yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta ayyukan makarantu a fadin jihar Kaduna.

 

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Dokta Hadiza Balarabe ce da ta wakilce shi, ta bayyana cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko sosai wajen gyara ajujuwan da suka lalace da kuma inganta ilimin malamai domin samar da ingantacciyar al’umma jihar.

 

Malam Uba Sani ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna tana yin duk mai yiwuwa wajen ganin an sanya kowane yaro a makaranta, ya ci gaba da zama a makaranta da kuma samun ingantaccen ilimi.

 

“Kokarin da muka yi ya bayyana a kan gina sabbin ajujuwa dubu 2,326 zuwa yanzu, wanda zai dauki dalibai 93,040 cikin kwanciyar hankali.”

 

“Mun samar da tebura masu kujeru biyu dubu 30,742, jimlar dalibai dubu 61,484 domin tabbatar da cewa dalibanmu sun yi karatu cikin jin dadi da kuma mutunci, wadannan makarantu kuma an tanadar musu da bandakuna masu tsafta da famfunan hannu na ruwan sha, wanda hakan ke nuna kudurinmu na tabbatar da cikakken tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya. muhallin koyo karatu”

 

A nasa jawabin, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna, Mista Tijjani Abdullahi, ya nuna cewa, kaddamar da rukunin gine gine 2 masu ajujuwa 12 kowanne a makarantar Rafin Guza, wani gagarumin ci gaba ne da gwamna Uba Sani ya samu wajen ciyar da bangaren ilimi gaba a jihar Kaduna.

 

Mista Abdullahi wanda ya samu wakilcin jami’in kula da ayyukan ci gaba na dindindin, Mubarak Mohammed ya bayyana cewa gina sabbin ajujuwan ya nuna yadda suka sadaukar da kansu wajen daukaka matsayin ilimi.

 

Ya ce kayayyakin ajujuwa ba wai kawai za su inganta yanayin koyo ga yara ba, har ma za su zama tushe na nasarorin da za su samu a nan gaba.

 

Mista Tijjani Abdullahi ya yi nuni da cewa, makarantar furamaren daya ce daga cikin manyan makarantun da jihar ke da su mai yawan dalibai dubu 7,160 da kuma ajujuwa 52, wannan da wasu dalilan ne da ya sa Gwamnan ya ga ya dace a gina karin ajujuwa 24 domin inganta ingancin koyarwa da koyo.

 

Mataimakiyar gwamnan ta samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati.

 

 

COV/AMINU DALHATU/Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara