Fasaha
Za Mu Hukunta Duk Wanda Aka Samu Yana Cin Zarafin Almajirai – Hukumar Almajirai Ta Kasa
Sakataren zartarwa na Hukumar Almajirai ta kasa Dr Muhammad Sani Idris ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu yana cin zarafin Almajirai a kowane bangare na kasar nan.
Dr Mohammad Sani Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wani yaro Almajiri da ake zargin an zalunce shi kuma yana jinya a Asibitin kasi da ke Dala Kano.
Ya ce gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ba a ci zarafin yara da ba su zuwa makaranta da kuma Almajirai ba.
Dokta Mohammed Sani Idris ya ce makasudin ziyarar tasa shi ne don jajanta wa yaron da iyalansa, da kuma sanar da jama’a cewa za a hukunta wanda ya aikata wannan danyen aikin don tabbatar da adalci.
Sakataren zartaswar ya bayyana cewa hukumar za ta bi diddigin lamarin domin ganin an hukunta wanda ya aikata hakan kamar yadda doka ta tanada.
Dakta Mohammad Sani Idris ya ci gaba da cewa hukumar ta himmatu wajen inganta Almajirai da kuma ba da ilmin makarantu da nufin ganin yadda harkar barace-barace da kuma rashin zuwa makaranta Yara sun zama tarihi.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati mai ci ta himmatu wajen magance kalubalen da ‘ya’yan Almajirai ke fuskanta a kasar nan.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
