Labarai
Kotu Ta Tura Wanda Ya Kona Masallata A Kano Zuwa Gidan Yari
Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare mutumin nan da ake zargi da cinna wa wasu mutane wuta a yayin da suke sallah a garin Larabar Abasawa a yankin Karamar Hukumar Gezawa.
Mai gabatar da kara, Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Sharia, Barista Haruna Isa Dederi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargi mai suna Shafiu Abubakar Gadan, ya zuba man fetur sannan ya cinna wuta a kan wasu mutane da ke yin sallar asuba a jam’i a masallacin da ke garin Gadan a yankin Karamar Hukumar Gezawa, lamarin da ya janyo da yawa daga cikin masallatan suka kone yayin da wasu suka mutu.
Bayan karanto masa takardar tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa aikata laifukan da ake zargin sa da shi na barna da samar da mummunan rauni da kisan kai bisa ganganci.
Sai dai lauyoyi sun nemi a sama wa wanda ake tuhumar lauyan da zai kare shi.
Alkalin kotun, Mai Sharia Halhalatulhuza’i Zakariyya, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2024 don sake gurfanar da shi.
Haka kuma alkalin ya amince da a sama wa wanda ake tuhumar lauyan da zai ba shi kariya duba da girman laifin da ake tuhumar sa da shi wanda idan ya tabbata hukuncinsa shi ne kisa
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
