Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda A Kano Ta Haramta Bukukuwan Hawan Sallah A Kano
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah.
Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar.
Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki matakan kariya tun kafin lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
“An shawarci masu ibada da su kasance masu bin doka da oda tare da gudanar da bukukuwan cikin lumana. Rundunar ta fitar da wasu ƙa’idojin tsaro da suka haɗa da: hawan doki wato (Kilisa),da tseren motoci ko tuki cikin ganganci da hatsari, da mallakar bindiga ko wani makami ba bisa ka’ida ba ko nuna su a fili, da kuma ɗaukar kaya marasa amfani ko masu haɗari da ka iya jawo shakku ko firgici.
Rundunar ta shawarci iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu, su guji shiga cikin ayyukan bata-gari ko baragurbi.
Rundunar ta kuna sha alwashin aiwatar da doka ba tare da rangwame ba.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
