Connect with us

Ilimi

ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu A Kaduna

Published

on

ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout

Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta.

Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa, ana aiwatar da shirin ne karkashin kulawar Ma’aikatar Ilimi ta jihar tare da hadin gwiwar kungiyoyin Save the Children da UNICEF.

“An samu kudade daga bashin sauki da tallafin da Bankin Raya Kasashen Musulmi (Islamic Development Bank) ya bayar domin aiwatar da wannan shiri,” in ji shi.

Mr. Angai ya ce, Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu bashin sauki da tallafi domin magance matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.

Ya kara da cewa, shirin zai gina sabbin makarantu guda 102 tare da gyara wasu 170 da ke aiki a yanzu, inda ake sa ran samun kimanin yara 200,000 da ba sa zuwa makaranta a kan gaba a cikin shekara hudu a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

Shi ma da yake jawabi, Jagoran Save the Children a jihar, Malam Tanko Mohammed Langaya, ya bayyana cewa shirin ROOSC yana da kudurin raba kayan koyon karatu da koyarwa sama da 500,000 ga dalibai a makarantu a matsayin wani muhimmin bangare na aiwatar da shirin.

“Wadannan kayan karatu ba wai na kari ba ne kawai, su ne tushen ilimi mai nagarta. Tabbatar da cewa kowane yaro yana da kayan karatu masu dacewa da shekarunsa da al’adarsa da kuma masu jan hankali, muhimmin mataki ne wajen samar da ingantaccen daidaito da ilimi ga kowa da kowa a Jihar Kaduna.”

Ko’odinetan shirin daga Save the Children, Mr. Emmanuel Mbursa, ya jaddada muhimmancin raba kayan karatu guda 100,000, yana mai cewa hakan babbar nasara ce a kokarin dawo da yaran da suka daina zuwa makaranta cikin tsarin ilimin gargajiya.

Ya kuma bayyana bukatar samun goyon bayan al’umma domin dorewar shirin.

A nasa jawabin, Daraktan Tsare-tsare a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Mista Salisu Bala, ya ce shirin na ROOSC yana da nufin bai wa yara ‘yan shekaru 6 zuwa 11 da matasa ‘yan shekaru 12 zuwa 18 da ke wajen makaranta damar samun ilimin firamare mai inganci.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Gudanar da Makarantun Firamare SBMC na Kaduna South, Alhaji Usman Sani, wanda kuma shi ne Hakimin Badikko, ya jaddada rawar da ilimi ke takawa wajen magance matsalolin rashin tsaro da matsin tattalin arziki a kasar.

Ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma da su tabbatar cewa dukkan yara masu shekaru na zuwa makaranta suna halartar makaranta, yana mai bayyana damuwa kan rashin isasshen samun ilimin yara kanana a wasu yankunan jihar.

Alhaji Usman Sani ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa kudurinsa na samar da ilimi ga kowa da kowa, yana mai cewa shirin ROOSC wata babbar hanya ce ta tabbatar da ingantacciyar makoma ga yaran Jihar Kaduna.

A halin yanzu, kananan hukumomi tara aka riga aka zaba domin rabon kayan koyon karatu. Sun hada da: Kaduna South, Igabi, Kaduna North, Sabon Gari, Soba da Lere.

Sauran sune: Kachia da Jema’a da kuma Kauru.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara