Labarai
Shugaba Tinubu Ya Karrama Bill Gates Da Lambar Girmamawa Ta CFR
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman.
Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa.

Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata.
Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate, ya ce karramawar da aka yi wa Mista Gates ta cancanta kwarai, idan aka yi la’akari da irin gagarumar rawar da ya taka a ci gaban Najeriya.
Farfesa Pate ya bayyana cewa taimakon da Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta bayar ya taimaka sosai wajen kawar da cutar shan inna (polio) a kasar.
Yayin da yake gode wa Shugaban Kasa bisa karramawar CFR, Mista Gates ya ce yaki da cutar shan inna daya ce daga cikin mafi wahala da Gidauniyarsu ta yi, sai dai hakan ya sa su hada kai da sarakunan gargajiya don cimma nasara.

Ya bayyana cewa Gidauniyar ta kaddamar da allurar rigakafin cutar HPB don rage mace-macen mata kimanin 7,000 a shekara sakamakon cutar sankarar mahaifa.
Mista Gates ya bayyana cewa allura guda daya kacal da ake bai wa ‘yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 na iya basu kariya na daga cutar.
Gates ya tabbatar wa Shugaban Kasa cewa zai ci gaba da jajircewa wajen inganta lafiya a Najeriya, inda ya ce yana da niyyar amfani da dukiyarsa gaba daya wajen wannan aiki cikin shekaru ashirin masu zuwa.
Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote, Ministan Harkokin Musamman da Hulda tsakanin Gwamnati, Zephaniah Jisalo, manyan jami’an Gidauniyar Gates, da Dakta Ayuba Burki Gufwan, Sakataren Gwamnati na Hukumar Kula da Masu Bukata ta Musamman na Kasa, na daga cikin wadanda suka halarci bikin karramawar.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
