Fasaha
Majalisar Nasarawa Ta Bukaci A Cire Malamai 1000 Daga Aikin Tantancewar Da Ake Yiwa Malamai
Majalisar dokokin jihar Nasarawa, ta umurci gwamnatin jihar da ta cire sabbin malamai 1000 wadanda ke karbar albashinsu daga aikin tantance malaman da ake yi a jihar.
Mataimakin kakakin majalisar Muhammad Adamu Oyanki, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake karanta kudurin majalisar bayan Daniel Ogazi ya kawo lamarin cikin gaggawa ga al’umma yayin zaman majalisar a lafiya.
Mohammed Adamu Oyanki ya ce malamai 1000 da ke karbar albashin na aiki ne bisa ka’idojin aikin gwamnati don haka ya kamata a cire su daga aikin tantancewar da ake yi a jihar domin samar da zaman lafiya, hadin kai da adalci.
Ya kuma umurci mashawarcin da ke gudanar da aikin tantancewar da ya mayar da wasikun daykar aiki da aka karbo ga malamai 1000 da ke kan lissafin albashin gwamnati nan take.
A cewarsa, wannan abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne, wadannan malamai 1000 sun samu aikin yi yadda ya kamata kuma suna karbar albashin watanni 9.
“Kudirin da majalisar ta yi shi ne, muna godiya ga mai girma Gwamna Abdullahi Sule bisa yadda ya dauki malamai aikin yi domin kara inganta harkar ilimi da kuma rage rashin aikin yi a jihar.
“Muna kuma umurtar mai ba da shawara da ya mayar wa malamai 1000 wasikun daukar da aka karbo nan take sannan su ci gaba da koyarwa, a biya su albashi” Inji shi.
“Kada wata hukuma ta dauki laifin wani, malamai 1000, kowa ya san ba su da laifi domin sun bi duk hanyoyin da suka dace don haka kada a ci zarafinsu, abin da muke yi shi ne kare gwamnati da doka.” Ya kara da cewa.
Mataimakin shugaban majalisar ya kuma kafa kwamiti na mutum shida wanda Daniel Ogazi zai jagoranta tare da shugaban kwamitin ilimi Abel Yakubu Bala tare da Luka Iliya Zhekaba a matsayin Sakatare da Barr. Esson Mairiga, Solomon Akwashiki da Muhammed Garba Isimbabi a matsayin membobi don kawo duk masu laifin da suka sayar da wasikun daukar aiki ga ’yan asalin jihar domin su samu.
“Wannan kwamiti zai kasance karkashin jagorancin Hon Daniel Ogazi tare da Hon. Luka Iliya Zhekaba, shugaban marasa rinjaye a matsayin sakataren kwamitin.
“Sauran mambobin sun hada da Hon. Solomon Yakubu Akwashiki, Hon. Mohammed Garba Isimbabi da Hon. Barr. Esson Mairiga” inji shi.
Mataimakin shugaban majalisar ya yi kira ga gwamna Abdullahi Sule da ya yi adalci tare da tausaya wa sauran malamai sama da 2000 da ba a biya su albashi ba.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
