Fasaha
WAEC: Daliban Taraba Sun Zauna Jarabawar Turanci Da Karfe 8:25 Na Dare
A wani lamari mai ban al’ajabi, a daren jiya dalibai a jihar Taraba sun zana jarrabawar kammala karatunsu na Ingilishi na WAEC da karfe 8:25 na dare, sama da sa’o’i 12 da fara sa’o’i 8:00 na safe.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jinkirin ya haifar da rudani da damuwa a tsakanin iyaye da masu kula da su, wadanda ke nuna shakku kan dalilan dage jarabawar da ba a taba ganin irinsa ba.
Lamarin dai ya yi matukar tayar da hankali idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin. Ba tare da wani bayani a hukumance daga WAEC ba, dalibai da iyaye suna mamakin abin da ya jawo tsaikon da kuma yadda hakan zai yi tasiri a ragowar jarabawar.
Wannan lamari da ba a saba gani ba ya haifar da tambayoyi fiye da amsoshi, kuma masu ruwa da tsaki suna dakon sanarwar hukuma daga WAEC domin fayyace lamarin.
KARSHE/JAMILA ABBA
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
