Ilimi
Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar biliyan 48 na aikin zaizayar Kasa
Jihar Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar sama da biliyan 48 don aikin kula da Makarantar ‘yan mata ta Mega dake Doma da kuma zaizayar kasa
Baya ga sanya hannu kan kwangilar, an kuma bayar da cak don biyan diyya ga mazauna yankin mai nisan mita 10 da ke kan hanyar aikin.
Da yake jawabi a wurin rattaba hannu kan kwangilar a hukumance a Hayin Missau Bogo, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da muhallin Gombe da kuma kare makomar jama’a.
A cewarsa aikin ba wai kawai zai shawo kan zaizayar kasa ba ne zai dawo da fata ga al’ummomin da abin ya shafa.
Alh. Inuwa Yahaya wanda ya bada umarnin kammala aikin a cikin watanni 30 ya bukaci dan kwangilar da ya gabatar da aiki mai inganci.
Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da juna a tsakanin al’umma, da kuma kiyaye ayyukan da ba su dace ba kamar sare itatuwa da zubar da shara da ke cutar da muhalli.
Shima da yake jawabi kwamishinan albarkatun ruwa da muhalli da gandun daji na jihar Gombe Mal. Muhammad Fawu, ya yabawa hadin gwiwar da gwamnatin Gombe da Bankin Duniya suka yi wajen samar da kudaden aikin, ya ce wani gagarumin kokari ne na kare muhalli da kuma tabbatar da makomar al’umma.
KARSHEN HUDU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
