Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince Da Sabbin Kwamishinoni Biyu
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da mutum biyu da Gwamna Uba Sani ya aike da sunayen su a tantance su a matsayin Kwamishinoni.
A cikin wata wasika da Gwamna Uba Sani ya aikawa Majalisar Dokokin, ya bukaci a amince da Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimin sai kuma Barrister Gloria Ibrahim a matsayin Kwamishinar Matasa da cigaban jihar.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, RT. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka amince da su, su yi amfani da kwarewar su domin farfado da bangaren Ilimi da bunkasa ci gaban matasa.
Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tantancewa da amincewa da shi a matsayin Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo ya lashi takobin gudanar da sauye-sauye a bangaren Ilimi ta hanyar fadada damarmaki, da yin garambawul a gine-gine da kuma inganta sha’anin koyarwa a makarantun dake fadin Jihar Kaduna.

Haka nan ita ma Barr. Gloria Ibrahim ta bayyana kudirinta na aiwatar da hangen nesa na Gwamna Uba Sani, na shigar da matasa cikin harkokin Mulki da ci gaba, sannan ta sha alwashin yin aiki tukuru wajen samar da damarmaki ga matasan dake fadin Jihar Kaduna.
Shamsuddeen Mannir Atiku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
