Labarai
Manufar Zuba Jari A Bangaren Sufuri Ita Ce Rage Cinkoso – Gwamnatin Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samar da hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan aikin samar da hanyoyi da motocin sufuri na zamani wato BRT da aka gudanar a Kaduna.
Aikin samar da hanyoyi da motocin sufuri na zamani yana da nufin inganta zirga-zirgar ababen hawa a birane da rage cunkoso da kuma inganta rayuwar jama’ar Jihar Kaduna.

Kwamishina Ma’aikatar Aiyyuka da Ababen More Rayuwa, Ibrahim Hamza ya tabbatar da kudurin gwamnati na sauya fasalin harkar sufuri da nufin ƙara bunƙasa tattalin arziki da jin daɗin al’umma.
Ya bayyana cewa aikin BRT wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati na inganta harkokin sufuri a faɗin jihar.
A nasa jawabin, Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Sufuri ta Jihar Kaduna, Injiniya Inuwa Ibrahim, ya ce tsarin BRT wani babban ci gaba ne da zai magance matsalolin sufuri da ke addabar jama’a.
Ya kuma shawarci mahalarta taron su yi nazari mai zurfi kan matsalolin da ake fuskanta tare da samar da mafita domin sauƙaƙa rayuwar fasinjoji.
A nasa ɓangaren, jagoran ƙungiyar Rebel Artic Joint Venture, Ted Regino, ya bayyana cewa kamfaninsu ne ke da alhakin kula da masu aikin, inda ya tabbatar wa al’ummar Kaduna da ingantaccen aiki mai sauri da nagarta.
Mai Kula da wannan taron Injiniya Emmanuel Oche John, ya ce suna tabbatar da cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun samu cikakken bayani kan aikin.
Wani mahalarci taron kuma Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa reshen Jihar Kaduna (NARTO), Alhaji Babangida Jafaru, ya bayyana cewa aikin BRT zai taimaka wajen warware matsalolin sufuri da ake fama da su a jihar.

Taken taron shi ne: “BRT a matsayin Kayan Aiki sufurin jama’a mai dorewa a Zamanin nan na Fasaha,” inda aka gayyato wakilai daga NURTW, FRSC, KASTELEA da sauransu.
Cov/Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
